Janar Dambazau Zai Tona Asirin Wadanda Su ka so Ayi wa Jonathan Juyin-mulki a 2010
- Janar Kukasheka Usman ya bada labarin abin da ya faru bayan mutuwar Ummaru ‘Yaradua
- Tsohon Sojan yace an samu wadanda suka zuga Janar Abdulrahman Dambazau ya shirya juyin mulki
- Dambazau bai karbi wannan shawara ba, ya kyale Goodluck Jonathan ya zama Shugaban Najeriya
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Tsohon mai magana da yawun sojojin kasa, Janar Kukasheka Usman (mai ritaya), ya bude wani boyayyan faifai game da Janar Abdulrahman Dambazau.
This Day ta rahoto Birgediya Janar Kukasheka (mai ritaya) yana cewa an taso Janar Abdulrahman Dambazau a lokacin yana hafsun sojojin kasa, ya yi juyin-mulki.
Tsohon sojan yake cewa bayan rasuwar Umaru Yar’Adua a 2010, wasu sun bukaci sojoji su kifar da Goodluck Jonathan, amma Janar Dambazau bai yi hakan ba.
Kukasheka ya yi wannan bayani ne a wajen bikin shekara-sheka da jaridar Blueprint Newspapers ta shirya. A taron 2022, an tattauna ne a kan batun rashin tsaro.
A cewar Kukasheka, kasashen Duniya sun samu labarin halin da ake ciki lokacin, inda Dambazau ya yi masu alkawari ba zai taba biyewa makiyan Najeriya ba.
An tunkari COAS ya kifar da Gwamnati
Kamar yadda tsohon jami’in ya fada, wasu makiyan kasa, sun bukaci sojoji su karbe gwamnati bayan shugaban kasa ya mutu, amma Dambazau bai amince ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A yayin da Abdulrahman Dambazau yake shugaban sojojin kasa, Kukasheka yace shi ne jami’in hulda da jama’a a ofishin COAS, don haka a duk rana su na tare.
A sa’ilin ne wasu suka ba shi shawarar ya karbe mulki ta hanyar kifar da gwamnati, Kukasheka ya bada shawarar Dambazzau ya kama sunansu a littafin tarihinsa.
"Yaushe za a juya gwamnati"
“A lokacin da mu ka ziyarci asibitin sojoji na 44 a garin Kaduna, mutane suna tambayar mu yashe za a bada sanarwar kifar da gwamnati.
GOC na Dakarun da ke Jos, Janar Akinyemi yana da rai, za a iya zuwa domin a tambaye shi.”
- Kukasheka Usman
Kiran waya kurum ya rage Janar Abdulrahman Dambazau ya yi domin sojoji su yi juyin-mulki, hafsun ya zabi a bar farar hula su cigaba da shugabancin kasar.
Gwamnoni sun halarci taron
Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni ya yi karin jawabi a wannan taro, yake cewa babu dalilin a burin wani mahaluki zai jefa daukacin al’ummar kasar nan a hadari.
Rahoton da Arise ta fitar ya nuna Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya tofa albarkacin bakinsa a taron, yace za iya magance matsalar tsaro a watanni shida.
Yaminu E. Musa zai rike NCTC
Labari mai zafin da ya zo mana shi ne an samu sabon shugaba a cibyar National Counter Terrorism Centre (NCTC) ta Najeriya da ake sa ran za ta yaki ta’addanci.
Femi Adesina yace Rear Admiral Yaminu E. Musa (rtd) shi ne wanda zai fara rike shugabancin NCTC.
Asali: Legit.ng