Yadda Zaku Gane Saurayi Na Zabga Muku Karya, Mawakiya Yemi Alade Ta Budewa Mata Sirrin

Yadda Zaku Gane Saurayi Na Zabga Muku Karya, Mawakiya Yemi Alade Ta Budewa Mata Sirrin

  • Fitacciyar mawakiya 'yar Najeriya, Yemi Alade, ta bayyana wata satar amsa ga mata kan yadda zasu bankado duk namijin dake zabga musu karya
  • Mawakiyar Najeriyan a wallafar da ta fitar, tace duk namijin dake lashe lebensa kafin yayi magana, ta yuwu karya yake zugawa mace
  • Wannan satar amsan ta Yemi kuwa ta tada kura inda masoyanta suka dinga martani a sashin tsokaci na wallafar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Fitacciyar mawakiyar Najeriya kuma mai rubuta waka da kanta, Yemi Alade, ta shiga kanun labarai kan wani satar amsa da ta bai wa 'yan mata.

A gajeriyar wallafar da tayi a shafinta na soshiyal midiya, tauraruwar mawakiyar tace duk namijin dake lashe lebensa kafin yayi magana ta yuwu karya yake zugawa.

Yemi Alade
Yadda Zaku Gane Saurayi Na Zabga Muku Karya, Mawakiya Yemi Alade Ta Budewa Mata Sirrin. Hoto daga @yemialade
Asali: Instagram

A yayin wallafa kyawawan hotunanta a shafinta na Instagram, Yemi Alade tace:

"Idan yana lashe lebe kafin yayi magana... Ta yuwu karya yake zabgawa."

Kara karanta wannan

Shawari kyauta: Hanyoyi 15 da za ku bi domin kiyaye kanku daga fadawa matsala a Najeriya

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ga wallafar:

Masoyan Yemi Alade sun yi martani kan wallafarta

Legit.ng ta tattaro muku wasu daga cikin tsokacin mabiya da masoyan mawakiyar. Ga wasu daga cikinsu:

ismeeddy:

"Na gode Allah da kika ce kila."

atabisco237:

"Ina kaunarki, amma banda tsokaci, ni ne tsokacin."

iamjinial:

"Sanar da ni wani abu akan hakan."

andcheal:

"Idan fa na fitar da harshena kadan na yi kasa da sama da shi kafin in ce wani abu?"

Bidiyon Kyakyawar Baturiya da Gudu Tana bin Matashi Bakar Fata don ta Karba Lambarsa

A wani labari na daban, wani matashi bakar fata ya hadu da wata kyakyawar budurwa baturiya kuma ya yanke hukuncin taya ta a karon farko cike da dabara da kwarewa a soyayya.

Ya tunkari budurwar ta bayanta inda ya taba ta a kafada tare da bata kyautar kyakyawar balan-balan.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari: APC ta gyara kasar nan, kamar ba a taba ta'addanci ba

Kyakyawar budurwar ta karba ba tare da bata lokaci ba, amma ba a hakan aka tsaya ba. Matashin ya durkusa da guiwarsa a kasa tare da sumbatar hannunta yayin da ta mika masa babu jinkiri a cikin jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng