Karon Farko a Tarihi, Buhari Ya Kirkiro Sabon Mukami Domin Magance Rashin Tsaro
- Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Yaminu E. Musa ya zama wanda zai jagoranci NCTC
- Rear Admiral Yaminu E. Musa mai ritaya ya dade yana makamancin wannan aiki a karkashin ONSA
- Tsohon sojan ya kware wajen harkar yaki da ta’addanci, ya wakilci Najeriya a majalisun Duniya
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - A makon nan ne Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Yaminu E. Musa a matsayin shugaban cibiyar NCTC da aka kafa.
Mai taimakawa shugaban Najeriyan wajen hulda da kafafen sadarwa na zamani, Bashir Ahmaad, ya bada wannan sanarwa a shafin Twitter.
Kamar yadda Bashir Ahmaad ya wallafa, Rear Admiral Yaminu E. Musa mai ritaya zai jagoranci wannan sabuwar cibiya da aka kafa a Najeriya.
Tsohon sojan saman shi ne zai fara rike cibiyar ta NCTC wanda za ta hada kan duka bangarori na jami’an tsaro da nufin a magance ta’addanci.
The Cable tace an fito da wannan cibiya ne a shekarar 2012, tun lokacin ta na aiki a karkashin ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro.
Wannan karo NCTC ta samu cin gashin kan ta, don haka aka nada mata cikakken shugabanta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar Femi Adesina
Asalin jawabin nadin mukamin ya fito ne daga bakin Femi Adesina, wanda yana cikin masu magana da yawun shugaba Muhammadu Buhari.
Sanarwar take cewa tsohon sojan zai kama aiki ba tare da bata lokaci ba, wa’adinsa na farko zai kare a shekarar 2027, zai yi shekaru bakwai a ofis.
Wanene Rear Admiral Yaminu E. Musa (rtd)?
A jiya Premium Times ta rahoto Femi Adesina yana cewa Yaminu Musa ya rike Darekta a bangaren yaki da ta’addanci a ofishin ONSA tun 2017.
Shugaban na NCTC ne yake da hannu wajen gyara tsarin yaki da ta’addanci na NACTEST, kuma a dalilinsa ne gwamnati ta iya fito da tsarin PCVE.
Bugu da kari, Musa ya kasance wakilin Najeriya a taron GCTF na Duniya, inda ake kokarin yaki da ta’addani, ya yi shekaru uku a wannan matsayi.
Matsalar tsaro a Kaduna
An ji labari Shehu Sani wanda ya yi Sanata na wa’adi daya a majalisar dattawa, ya zargi Nasir El-Rufai da taimakawa matsalar rashin tsaro a Kaduna.
Shehu Sani yace ya yi kokarin ankarar da gwamnati a baya, amma Gwamna ya yake shi, sannan ya rika yin kalaman da suka jefa al'umma cikin hadari.
Asali: Legit.ng