Gwamna Ganduje Ya Kafa Kwamitin da Zai Binciki Jami'ar da Kwankwaso Ya Gina a Kano

Gwamna Ganduje Ya Kafa Kwamitin da Zai Binciki Jami'ar da Kwankwaso Ya Gina a Kano

  • Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya kafa kwamiti da zai gudanar da bincike kan sulalewar wasu kuɗaɗe a KUST Wudil
  • Gwamna ya yi haka ne biyo bayan ɓatan wasu kuɗi kimanin miliyan N353m na ma'aikatan Fansho a jami'ar
  • Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ne ya kafa Jami'ar a shekarar 2000 lokacin Ganduje na mataimaki

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya kafa kwamitin bincike da zai yi nazari kan abubuwan da tawagar ziyara ta bankaɗo a ɗaya ɗaga cikin jami'o'in da ke ƙarƙashin jihar.

Daily Trust ta ruwaito cewa kwamitin da ya kai ziyara jami'ar kimiyya ta fasaha ta Kano (KUST) dake garin Wudil ya baiwa gwamnati shawarwari kan abubuwann da ya gano a rahotonsa.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Kano.
Gwamna Ganduje Ya Kafa Kwamitin da Zai Binciki Jami'ar da Kwankwaso Ya Gina a Kano Hoto: Gandujiyya Online/facebook
Asali: Facebook

Tuni gwamnatin Kano karkashin gwamna Ganduje ta fara aiwatar da wasu shawarwarin, wanda a cikin su har da bukatar gwamnatin ta gudanar da bincike.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Jigon Jam'iyyar APC Kuma Shugaba, Musa Abubakar, Ya Rasu a Hanyar Kano

A rahoton tawagar da ta kai ziyara KUST, sun nemi a yi bincike kan yadda ake tafiyar kuɗaɗen makarantar biyo bayan gano cewa an karkatar da wasu kuɗin Fanshon ma'aikata da ya kai miliyan N352m.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai, Malam Muhammad Garba, ya fitar ya ce kwamitin da gwamna ya kafa yanzu, zai bi ba'asin baki ɗaya yadda kuɗaɗe ke zurare wa a jami'ar.

Haka zalika, kwamishinan ya ƙara da cewa kwamitin zai kuma duba yadda harkokin Audita ke tafiya kana ya dawo da duk wasu kuɗi da aka karkatar.

Mutanen da suka shiga kwamitin

A cewar kwamishinan, kwamitin zai gudanar da aikinsa ne karkashin jagorancin babban sakatarem ma'aikatar ƙaddamar da ayyuka, Ofishin shugaban ma'aikatan jihar Kano.

Sai kuma mambobi da suka haɗa da, Babban Sakataren hukumar REPA, ofishin sakataren gwamnati, babban Sakataren hukumar Fansho, babban sakataren Ma'aikatar kuɗi da Audita Janar na jihar Kano.

Kara karanta wannan

Ana Kokarin Sasanta Atiku da Wike, Jiga-Jigan PDP da Daruruwan Mambobi Sun Suaya Sheka zuwa APC

Sauran mambon sune; shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rasahawa ta jiha, babbam Sakataren ma'aikatar ilimi, yayin da babban Sakataren ma'aikatar Shari'a zai rike Sakataren kwamiti.

Kwamishinan ya ce gwamna Ganduje zai kaddamar da kwamitin domin ya kama aiki gadan-gadan a wata rana da za'a ranar nan gaba.

A wani labarin kuma Gwamna Ganduje Ya Aike Da Sunayen Sabbin Kwamishinoni 8 Majalisar Dokoki

Gwamnan jihar Kano ya naɗa sabbin kwamishinoni Takwas, ya tura da sunayen su ga majalisar dokoki domin tantance wa.

A zaman majalisar na yau Litinin, Kakaki ya karanta sunayen mutanen, waɗan da zasu maye gurbin tsoffin da suka yi murabus.

Asali: Legit.ng

Online view pixel