"A Taimaka min Don Allah, Ina Neman AIkin Yi," Makaho mai Kwalin NCE Ya Koka

"A Taimaka min Don Allah, Ina Neman AIkin Yi," Makaho mai Kwalin NCE Ya Koka

  • Wani matashin Najeriya mai fama da makanta mai suna Hamza Aminu Abdullahi, ya koka ga 'yan Najeriya da su taimaka masa da aikin yi
  • Kamar yadda mawallafi Jaafar Jaafar ya sanar a shafinsa ba Facebook, Hamza yana da kwalin NCE inda ya karanci karatu na musamman da na'ura mai kwakwalwa
  • Ba da makanta aka haifa Hamza ba, ya rasa idanunsa ne a shekarar 2006 kuma a haka ya kokarta har ya kammala NCE amma yanzu yana neman aiki

Wani matashi 'dan Najeriya ya koka ga jama'a kan neman aikin da yake yi bayan ya kammala karatunsa na NCE.

Matashin mai suna Hamza Aminu Abdullahi yana da kwalin NCE a bangaren karatu na musamman da na'ura mai kwakwalwa.

Makaho mai ilimi
"A Taimaka min Don Allah, Ina Neman AIkin Yi," Makaho mai Kwalin NCE Ya Koka. Hoto daga Jaafar Jaafar
Asali: Facebook

Hamza yana da kwalin NCE

Hamza ba shi da idanu kuma ya kasa samun aikin yi tun bayan da ya kammala karatunsa.

Kara karanta wannan

Ka bar ni na more: Uba ya damu da yadda dansa yake hana shi jin dadin aure

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ba a makance aka haifa Hamza ba, ya rasa idanunsa ne a 2006 amma duk da haka yayi kokarin kammala karatunsa.

A yayin wallafa labarinsa a Facebook, Jaafar Jaafar ya rubuta:

"Hamza Aminu Abdullahi ya rasa idanunsa a 2006. Duk da wannan kalubalen, ya kammala karatunsa na sakandare kuma ya samu har ya yi NCE a fannin karatu na musamman da na'ura mai kwakwalwa a 2017. Tun bayan nan, ya dinga neman aiki amma babu nasara."

Yayi kira ga duk wanda ke son samarwa Hamza da aikin yi da ya kira shi kan wannan lambar: 07061659483

Kaunar da Nake wa 'Yan Najeriya Bata Misaltuwa, Shugaba Buhari

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake jaddada burin mulkinsa na Inganta rayuwar 'yan kasa duk da matsin tattalin arzikin da ake fama da shi.

Kara karanta wannan

Musa Sani: Dan Najeriya Mai Shekaru 13 Ya Sake Kera Wata Gadar Sama, Hotunan Sun Yadu

Ya ce burinsa na inganta rayukan 'yan Najeriya bai dishe ba, inda yake kira da 'yan Najeriya da su kara hakuri, jaridar Daily Nigerian ta rahoto.

Shugaban kasan ya bayar da tabbacin hakan ne lokacin da ya karba bakuncin tsohon shugaban tsohuwar jam'iyyar CPC a gidan gwamnati a Abuja, ranar Talata.

Ya kara da kira ga shugabannin siyasa da su mayar da hankali wurin tabbatar da sun daga darajar kasar nan.

Shugaban kasan yace son kan da ya janyo rashin miliyoyin rayuka tsakanin 1967 zuwa 1970 bai kamata a bari ya maimaita kansa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng