Shehu Sani: Yadda Gwamna El-Rufai Yake Taimakawa Wajen Jawo Matsalar Tsaro
- Shehu Sani ya yi tsokaci game da kokawar da Nasir El-Rufai yake yi a kan matsalar rashin tsaro
- ‘Dan siyasar yace duk sai da ya yi irin wannan maganganu a baya, amma Gwamna ya yake shi
- Yanzu ana maganar yau ‘Yan ta’adda suna kokarin karbe iko a wasu yankunan da ke jihar Kaduna
Kaduna - Shehu Sani wanda ya yi Sanata na wa’adi daya a majalisar dattawa, ya zargi Nasir El-Rufai da taimakawa matsalar rashin tsaro a jihar Kaduna.
Shehu Sani ya zanta da gidan talabijin Arise TV a ranar Lahadi, 14 ga watan Satumba 2022, aka tabo batun wasikar da Gwamnansa ya aikawa shugaban kasa.
Sanata Sani yace Gwamna Nasir El-Rufai ya shaidawa Duniya gazawarsa a wannan wasika da ya rubuta zuwa Aso Villa, bayan a baya ya yi ta boye matsalar.
A cewar ‘dan siyasar, a cikin koke-koken da El-Rufai ya yi wa shugaba Muhammadu Buhari, babu wani sabon abin da ba a ankarar da gwamnati tun baya ba.
Sani yace a lokacin da ya bijiro da matsalar a majalisa, El-Rufai ya nuna ana zuzuta lamarin, sai ga shi yau ana kukan ‘yan ta’dda na neman kafa gwamnati.
Akwai laifin Gwamnonin Arewa
Premium Times ta rahoto tsohon Sanatan yana zargin Gwamnonin Arewa ta yamma da kin daukar mataki a lokacin da ya kamata wajen kawo zaman lafiya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Shahararren ‘dan gwagwarmayar ya kuma zargi gwamnoni da kin kashe kudi da nufin magance matsalolin rashin tsaro da talakawansu suke fuskanta.
A wasu jihohin, gwamnoni na kashe kudinsu wajen taimakawa jami’an tsaro domin yakar ta’addanci, Shehu Sani yace gwamna El-Rufai ba ya yin irin haka.
“Gwamnatin Kaduna ba tayi kokari sosai wajen magance rashin tsaro ba, kuma babu kwakkwaran gudumuwar da ake ba jami’an tsaro da ke jihar.
Inda El-Rufai ya yi kuskure - Shehu Sani
“Sannan irin kalaman da Mai girma yake yi, sun jawo ‘yan ta’dda sun dawo Kaduna.”
- Shehu Sani
A cewar Shehu Sani, duk da gwamnoni ba su da iko da jami’an tsaro a dokar kasa, za su iya bada gudumuwarsu ta hanyar tallafawa sojoji da ‘yan sanda.
A halin da ake ciki, Sanatan yace kananan hukumomin Kaduna ta Arewa da na Kaduna ta Kudu kadai ake zaman lafiya duk da tarin dakaru a jihar
Cikas a Yaki da Ta’addanci
An ji labari Sanatan jihar Borno, Muhammad Ali Ndume yana da ra’ayin cewa rashin kayan fada na zamani ya hana ta’addanci ya zama tsohon labari.
An rahoto Ndume yana bada shawarar a sa dokar ta baci a bangaren tsaro. A karshe yace Ubangiji zai damke Muhammadu Buhari ne da laifi ba kowa ba.
Asali: Legit.ng