Babu Najeriya a Jerin Kasashen da Majalisar Dinkin Duniya Ta Ce Su Ne Duniya Ta Uku
Jerin kasashen da ba su ci gaba ba da Kwamitin Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta fitar ya nuna kasashen da ba sa ci gaba da kuma lokacin da kwamitin na duniya ya tattara bayanansu.
An fitar da jerin sunayen da kwamitin Majalisar Dinkin Duniya kan manufofin raya kasashe ya hada a karshen watan Nuwamban 2021.
A cewar kungiyar ta duniya, za a kara sabunta jerin lokacin da sabbin bayanai da bincike suka samu.
Ga dai jerin kasashen da shekarar da suka samu 'yancin kai:
- Afganistan - 1971
- Madagascar - 1991
- Angola 1-1994
- Malawi - 1971
- Bangladesh - 1975
- Mali - 1971
- Benin - 1971
- Muritaniya - 1986
- Bhutan - 1971
- Mozambique - 1988
- Burkina Faso - 1971
- Myanmar - 1987
- Burundi - 1971
- Nepal - 1971
- Cambodia - 1991
- Nijar - 1971
- Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya - 1975
- Rwanda - 1971
- Chadi - 1971
- Sao Tomé and Principe - 1982
- Comoros - 1977
- Senegal - 2000
- Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo - 1991
- Saliyo - 1982
- Djibouti - 1982
- Solomon Islands - 1991
- Eritrea - 1994
- Somalia - 1971
- Habasha - 1971
- Sudan ta Kudu - 2012
- Gambia - 1975
- Sudan - 1971
- Guinea - 1971
- Timor-Leste - 2003
- Guinea-Bissau - 1981
- Togo - 1982
- Haiti - 1971
- Tuvalu - 1986
- Kiribati - 1986
- Uganda - 1971
- Jamhuriyar Jama'ar Lao - 1971
- Jamhuriyar Tanzania - 1971
- Lesotho - 1971
- Yemen - 1971
- Laberiya - 1990
- Zambiya - 1991
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Watakila wasu su ji mamaki, amma dai Najeriya ba ta cikin jerin wadannan kasashe da ake yiwa kallaon marasa ci gaba duk da tabarbarewar tattalin arziki da ake fama dashi a kasar a 'yan shekarun nan.
Bankin Duniya Ya Lissafa Kasashen Afirka 34 da Ke da Tarin Bashi Kuma Ka Iya Samun Yafiya
A wani labarin kuma, a cewar wani rahoton Business Insider, akwai kasashe matsakata karfi 34 a Afirka da ke da dimbin basussuka akansu.
Jerin ya fito ne karkashin wani shiri na hadin gwiwa na Bankin Duniya da Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF).
An dai kaddamar da shirin ne a 1996. Bayanai daga asusun IMF na cewa, shirin na son tabbatar da cewa babu wata kasa matsakaiciya da za ta fuskanci nauyin bashin da ba za ta iya sarrafa kanta ba.
Asali: Legit.ng