Rashin tsaro: Sanatan APC Ya Fadi Tushen Matsala, Yace Gwamnati Ba ta Shirya ba
- Muhammad Ali Ndume ya na ganin duk inda ake shiga, dakarun sojojin Najeriya za su iya shiga
- ‘Dan majalisar yana ganin babban tasgaro da ake samu shi ne a samu kayan yaki irin na zamani
- Sanata Ndume ya ba Gwamnati shawara, ya kuma bukaci a maida hankali wajen kawo zaman lafiya
Abuja - Sanata Muhammad Ali Ndume yana da ra’ayin cewa rashin kayan fada na zamani ne ya hana ta’addanci ya zama tsohon labari a kasar nan.
Da aka yi hira da shi a shirin siyasa a tashar talabijin na Channels, Muhammad Ali Ndume, ya yi magana a game da rashin sha’anin tsaro a Najeriya.
Ndume mai wakiltar kudancin Borno a majalisar dattawa ya wanke sojoji daga zargi, yace rashin kayan aiki ya jawo har gobe ake fama da ‘yan ta’adda.
“Zan sake fada, amfanin gwamnati shi ne tsaro da walwalar al’ummarta. Babu isassun sojojin kasa a Najeriya.
Ba su da kayan aikin, ba su da fasahar zamanin da ake bukata domin su magance matsalolin da ake da su.”
- Muhammad Ali Ndume
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Menene amfanin gwamnati?
Sanatan yake cewa makasudin gwamnati shi ne ta kula da tsaro da jin dadin jama'a, yace idan aka samu zaman lafiya ne abubuwa za su yi kyau.
An rahoto Ndume yana bada shawarar a sa dokar ta baci a bangaren tsaro. A karshe yace Ubangiji zai damke shugaban kasa ne da laifi ba kowa ba.
Jigon na jam’iyyar APC ya bada shawarar cewa idan har za a ba jami’an tsaro wani aiki, zai yi kyau a tsaida wa’adin da ake so su kammala aikin.
“Kundin tsarin mulki na Najeriya ya yi bayani karara, amfanin gwamnati shi ne tsaro da walwalar al’ummarta.
Tun wuri zai fi kyau duka bangarorin gwamnati da mutanen Najeriya sum aida hankali kan kawo zaman lafiya.”
“Zan sake nanatawa, sojojin kasar nanza su iya fuskantar duk aikin da ke gabansu. Idan an ba su aiki, sai a ba yanke masu lokaci.”
- Muhammad Ali Ndume
A game da fasinjojin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja da ‘yan ta’adda suka fito da su, Daily Trust ta rahoto Ndume yana cewa sai da aka biya kudin fansa tukuna.
Siyasar 2023 ta karaso
A gefen siyasa, an ji labari tsohon Gwamna kuma jagora a jam’iyyar hamayya, Bode George ya gargadi Atiku Abubakar a kan takarar da za iyi a zaben 2023
George yace ba zai yiwu Wazirin na Adamawa ya zama Shugaban kasa har PDP ta koma Aso Villa, ba tare da ya samu kuri’un yankin Kudancin Najeriya ba.
Asali: Legit.ng