An Yankewa Kasurgumin Mai Garkuwa da Mutane Wadume Hukuncin Shekaru 7 a Magarkama
- Kotun Abuja ta yankewa wani kasurgumin dan bindiga hukuncin zaman gidan maza na shekaru bakwai
- Hamisu Baka na daya daga cikin 'yan ta'addan da suka addabi yankuna da dama a jihar Taraba
- An sha kame 'yan ta'adda a Najeriya ana daurewa, duk da cewa shari'ar na iya daukar tsawon lokaci
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
FCT, Abuja - Babbar kotun Abuja karkashin mai shari'a Binta Kyako ta yankewa kasugumin dan bindigan da ya addabi wani yankunan jihar Taraba.
Bayan shafe lokaci ana shari'a, an kama Hamisu Bala, wanda aka fi sani da Wadume da laifukan da ake tuhumarsa, kana aka daure shi zaman shekaru bakwai a gidan yari.
Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, Wadume zai yi zaman magarkama ne tare da wasu mutane biyu da ake tuhumarsu tare.
Rahoton Daily Trust ya ce, an yanke hukuncin ne a ranar 22 ga watan Yuli, amma aka sanar da manema labarai a yau Litinin 15 ga watan Agusta.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A baya an gabatar da tuhume-tuhume 13 kan Wadume, inda Nyako ta same shi da laifuka biyu.
Hakazalika, wani sufeton dan sanda zai yi zaman shekaru uku a gidan yari bisa laifin boye laifi da aka gabatar a gaban kotun.
Jami'an mai suna Ali Dadje, an ce yana aiki ne a ofishin 'yan sanda da ke karamar hukumar Ibi a jihar Tarana.
Baya ga daure dan ta'adda Wadume da Dadje, sauran tsagerun da aka daure su sun hada da Auwalu Bala (Omo Reza), Uba Bala (Uba Delu), Bashir Waziri (Baba Runs), Zubairu Abdullahi (Basho) da Rayyanu Abdul.
Sai dai, Nyako ta wanke tare sallamar Omo Razor da Baba Runs saboda shaidun da suka bayyana.
A bangare guda, Delu, Abdullahi da Abdul za su yi zaman shekaru bakwai a gidan kasa, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Yadda aka gurfanar dasu
An gurfanar da Wadume da sauran abokansa cin mushensa a gaban kotu bisa tuhumarsu da laifin satar mutane, kisa, ta’addanci da kuma mallakar muggan makamai.
Laifukan sun biyo bayan kashe wasu jami’an ‘yan sanda uku da wasu farar hula biyu a ranar 6 ga watan Agustan 2019 da wasu sojoji suka yi.
‘Yan sandan da ke cikin tawagar ‘Intelligence Response Team’ da ke Abuja, sun kama Wadume ne a Ibi kafin sojojin su yi musu kwanton bauna a kan hanya.
Evans: Ko Kaɗan Bai Nuna Alamar Nadama Ba Yayin Shari’arsa Na Shekaru Hudu, Alƙali
A wani labarin, alkali ta yanke hukunci ga wani mai garkuwa da mutane, Chukwudimeme Onwuamadike wanda aka fi sani da Evans, da sauran mutane biyu da aka kama da laifin garkuwa da Mr Donatius Dunu, shugaban Maydon Pharmaceuticals Ltd.
Alkalin babbar kotun Ikeja, Justice Hakeem Oshodi, ya yanke wa Evans da sauran mutane biyu hukuncin daurin rai da rai, inda yace basu nuna alamar nadana ba akan aika-aikar da suka yi duk da shaidun da aka gabatar akan su.
Gwamnatin Jihar Legas ta gurfanar da Evans da sauran mutane 5 a gaban kotu, Vanguard ta ruwaito.
Asali: Legit.ng