Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Yan Kwallon Najeriya Mata Guda Shida a Edo

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Yan Kwallon Najeriya Mata Guda Shida a Edo

  • Wasu miyagu sun sace mata 'yan kwallon kafa a Najeriya yayin da suke kan hanyar komawa Edo bayan murza leda
  • Wata majiya ta bayyana cewa masu garkuwa sun nemi iyalai sun tattara musu miliyan N5m kan kowace yar wasa ɗaya
  • Lamarin ya auku ne a yankin Uronigbe wanda ya kasance iyaka tsakanin jihar Edo da maƙociyarta Delta

Edo - Wasu yan kwallo mata a Najeriya masu tasowa sun shiga hannun yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne ranar Jummu'a a yankin Uronigbe, ƙaramar hukumar Orhiomwon, jihar Edo.

Tribune Online ta rahoto cewa an yi garkuwa da yan kwallon mata ne a wani gari da ke iyaka tsakanin jihohin Delta da Edo yayin da suke kan hanyar komawa gida bayan halartar wata gasar kwallo a jihar Delta.

Kara karanta wannan

Wasu Mutum Uku Sun Tsallake Rijiya da Baya a Hannun Mutane Bayan Asirin Su Ya Tonu a Abuja

Taswirar jihar Edo.
Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Yan Kwallon Najeriya Mata Guda Shida a Edo Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Wata majiya daga yankin da ta tabbatar da lamarin, ta ce masu garkuwan sun tuntuɓi iyalan yan kwallon, inda suka buƙaci a tattara musu miliyan N5m kan kowace mace ɗaya.

Punch ta rahoto Majiyar ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Sun je Owa-Aleru domin fafata wani wasan kwallo, a hanyarsu ta dawowa aka yi garkuwa da su a yankin Uronigbe, bodar jihar Delta da Edo.Waɗan da abun ya shafa sun haɗa da, Precious Agbajor, wata Abraham, Nancy, Beatrice, da direba."
"Su Shida ne ke hannun masu garkuwa. Tuni aka kai rahoton lamarin Caji Ofis ɗin Uronigbe. Yan bindigan sun tuntuɓi iyalan Agbajor kuma sun nemi ya biya miliyan N5m kuɗin fansar matarsa."

Wane mataki hukumomi suka ɗauka?

Legit.ng Hausa ta gano cewa hukumar yan sandan jihar Delta ta tabbatar da faruwar lamarin yayin da takwararta ta jihar Edo ta bayyana cewa har yanzu ba ta sami rahoto kan abun da ya auku ba.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Gamu da Cikas Yayin da Suka Yi Yunkurin Garkuwa da Basarake a Kano

Da yake tsokaci kan lamarin, kakakin hukumar yan sandan Delta, Bright Edafe, ya tabbatar da faruwar lamarin da cewa an sace matan ne a yankin jihar Edo.

Amma takwaransa na reshen jihar Edo, Chidi Nwabuzor, ya ce a iya abun da ke ƙasa a hukumar yan sandan jihar, babu wani bayani game da lamarin garkuwar.

"Kun sani cewa sun tura abubuwan da muka tattara zuwa Hedkwatar yan sanda ta ƙasa, babu wani rahoton kan haka a gaban mu."

A wani labarin kuma A cigaba da luguden wuta, Sojoji sun kai samame sansanin yan bindiga ta sama da Ƙasa, Sun Kashe Dandazonsu a Kaduna

Sojojin Sama da Ƙasa sun yi luguden wuta kan sansanin yan ta'adda a yankin karamar hukumar Chikun jihar Kaduna.

Kwamishinan tsaro, Samuel Aruwan, ya ce sojojin sun hallaka yan ta'adda da dama, sun kwato makamai da sauran su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262