WAEC 2022: Hazikan Dalibai 4 Da Suka Ci Jarrabawarsu Da Sakamakon A, Hotunansu Da Sakamakon
- Wata hazikar yarinya yar shekara 15, Ogunjobi Moyinoluwa Adekemi, ta samu A guda 8 da B daya a sakamakon jarrabawar WAEC
- A wani rahoton, wani mai aikin kwasar bola ya farantawa wadanda ke daukan nauyinsa rai inda shima ya ci jarrabawarsa ta WAEC
- Oluwole Oluwabukunmi shima ya shiga jerin hazikan dalibai a kasar da suka ci jarrabawarsu ta WAEC da A
Jarrabawar WAEC da hukumar Shirya Jarrabawar Manyan Makarantun Sakandare na Afirka ta Yamma ke shiryawa na cikin jarrabawar dalibai ke fargabar rubutawa a Afirka.
Shine jarrabawar da ke zama manuniya kan yadda dalibi zai cigaba da karatunsa na boko, hakan yasa ake bashi muhimmanci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A 2022, bayan hukumar jarrabawar ta fitar da sakamako, an rika jinjinawa wadanda suka ci A a darrusan. A wannan rahoton Legit.ng za ta haskaka fitila kan wasu dalibai hudu hazikai.
1. Ogunjobi Moyinoluwa Adekemi
Dalibar yar shekara 15 ta janyo hankalin dubban mutane ne bayan sakamakon jarrabawarta ya nuna ta samu A guda takwas da B daya.
Bugu da kari, ta rubuta JAMB na 2022 ta samu maki 351. Ta ci 97 a lissafi.
2. Wani yaro mai aikin kwasar Bola
Wani dan Najeriya mai suna Jibola, ya nuna yadda wani maraya da ya ke daukan nauyin karatunsa ya ci A biyu da B guda shida a WAEC.
Jibola ya ce ya yi murnar ganin bai yi asarar biya wa yaron kudin jarrabawa ba da na lesson.
Mutane da dama sun yaba tausayinsa. Ya yi alkawarin zai biya wa yaron kudin karatu a jami'a ya tabbatar ya fita da 1st class.
'Yan Sanda Sun yi Ram da Shugaban Dalibai Bayan Yace Minista Bai yi Wanka ba Ya Gana da Shugaban Kasa
3. Oluwole Oluwabukunmi
Wani yaro dan Najeriya ya nuna hazaka a jarrabawar, ya samu A dukkan darrusan da ya rubuta.
Ya sake maimaita abin sha'awar a JAMB inda ya samu maki fiye da 300.
4. Uchegbu Obinna John-Paul
Yaron dan shekara 16 ya samu A guda tara a jarrabawar da ya rubuta na WAEC. Sakamakonsa ya nuna ba a bar matasan Najeriya a baya ba.
Shima ya sake nuna basirarsa inda a ci maki 332 a JAMB.
Karfafawa masu hazaka gwiwa
Domin karfafawa yan Najeriya masu hazaka gwiwa, ya kamata a kafa wata gidauniya da za a rika karrama masu kwanya irin wadannan yaran a cikin mu.
Asali: Legit.ng