Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Kukan Yadda Ake Kashe Namun Daje Dake Harabar Gidan

Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Kukan Yadda Ake Kashe Namun Daje Dake Harabar Gidan

  • Hukumar Dake Kula Da Fadar Shugaban Kasa ta Nemi Yan Najeriya Su Daina Kashe Namun Daje Dake Harabar Aso Villa
  • Hana kashe namun daji al'ada ce na kare nau'in dabbobi da dajin da suke gudanar da rayuwar su a ciki da fadar gwamnati tarayya ta himatu ta kare su
  • Hukumar kula da gandun daji na kasa ta bayyana bakin cikin ta akan yadda wasu suka kashe wani katon Maciji a dajin fadar shugaban kasa

Abuja - Mahukuntar fadar shugaban kasa sun bayyana damuwarsu kan kisan da aka yi wa namun daji dake dajin fadar shugaban kasa da ke Abuja. Rahoton Sunnewsonline

Sakataren dindindin na gidan gwamnati, Tijjani Umar, ya yi magana a karshen mako yayin da yake karbar tawagar masu kula da gandun daji na kasa, da takwarorinsu a fadar shugaban kasa, wadda aka fi sani da ‘Royal Rangers’.

Kara karanta wannan

Abubakar Malami Ya ce an Kashe Duka Kudaden Da Aka Kwato Daga Barayin Gwamnatin Akan abubuwan Raya Kasa

Umar ya jaddada mahimmancin kare rayukan tsirraron dabbobi da wuraren zaman su na asali, kuma ya yi alkawarin bunkasa wuraren zaman namun daji ta hanyar daukar matakan da suka dace.

Villa
Hukumar Kula Da Fadar Shugaban Kasa Ta Nemi Najeriya Su Daina Kashe Namun Daje Dake Harabar Gidan FOTO Legit.NG
Asali: UGC

Umar ya kara da cewa dajin dake harabar fadar shugaban kasa gida ne ga wasu nau'ikan namun daji da suka hada da birai, kada, Manyan Macizai, kunkuru, berayen daji, tsuntsayen, jemagu da sauran su.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A nasu jawabin, Salihu Manzo, da Kehinde Abidemi, manyan Jami’an kula da gandun daji, , sun gode wa babban sakatare na dindindin kan yadda yake da sha’awar kare rayukan namun daji.

Manzo, ya bayyana takaicin sa akan kisan gillar da aka yi a wa wani katon maciji a dajin dake harabar fadar shugaban kasa inda ya ce hukumar su, zata kawo karshe kashe namun daji a kasar.

Dole Kujerar Shugaban Kasa ya Dawo Kudu a 2023 - Akeredolu

Kara karanta wannan

Jin dadin malamai: Jihohi 15 da suka gaza biyan malaman firamare karancin albashin N30K

A wani labari kuma, Jihar Ondo - Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredolu yayi ikrarin cewa dole kujerar shugabankasa ya koma yankin Kudu a 2023 saboda kada a saba yarjejeniyar mulkin karba-karba dake tsakanin yankunan kasar. Rahoton PUNCH

Mulkin karba-karba bayan cikin kundin tsarin mulkin Najeriya amma ana amfani da tsarin tun 1999 da mulki ya dawo hannun farar hula saboda haka bai kamata tsarin ya canza ba a yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa

Online view pixel