Yan Bindige Sun Yi Wa Yan Bijilante Kwanton Bauna, Sun Bindige 2 Har Lahira A Abuja

Yan Bindige Sun Yi Wa Yan Bijilante Kwanton Bauna, Sun Bindige 2 Har Lahira A Abuja

  • Yan bindiga da suka yi garkuwa da wani manomi sun halaka jami'an tsaro na bijilante biyu a birnin tarayya Abuja
  • Yan bijilanten sun tafi sansanin yan bindigan ne da nufin ceto wani Aliyu Musa da aka sace daga gonarsa amma yan bindigan suka musu kwanton bauna
  • Wani dan bijilante da ya ce sunansa Ishaku ya ce lamarin ya faru ne misalin karfe 4.30 na yammacin Alhamis kuma an yi wa wadanda suka rasu jana'iza

Abuja - Wasu mambobin kungiyar bijilante biyu sun mutu sakamakon gumurzu da suka yi da yan bindiga a garin Gasakpa a gundumar Gawu, karamar hukumar Abaji, Abuja, rahoton Daily Trust.

Wani mamban kungiyar yan bijilante mai suna Ishaku ya ce lamarin ya faru ne misalin karfe 4.30 na ranar Alhamis a wani daji da ke kan iyakar Abuja da jihar Niger.

Kara karanta wannan

Yan ta'ada Sun Kashe Yan Banga Biyu Yayin da Suka Musu Kwantar Bauna a Abuja

Abuja
Yan Bindige Sun Yi Wa Yan Bijilante Kwanton Bauna, Sun Bindige 2 Har Lahira A Abuja. Hoto: @daily_trust.

Ya ce yan bijilanten sun tafi dajin ne domin ceto manomi mai suna Aliyu Musa wanda aka sace shi a gona.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Isiyaku ya ce yan bijilanten suna daf da isa sansanin yan bindigan ne kwatsam suka bude musu wuta.

A cewarsa, an kashe mutum biyu cikin yan bijilanten sakamakon musayar wuta da suka yi, yana cewa an musu jana'iza.

Martanin yan sanda

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, DSP Adeh Josephine, bata riga ta amsa sakon tes da aka aika mata ba game da lamarin.

Daily Trust ta rahoto cewa a baya-bayan nan, yan ta'addan sun rika kai hare-hare a garuruwan Adagba, Gurdi, Paiko Bassa da Rafin Daji a karamar hukumar Abaji da ke da iyaka da kauyukan Jihar Niger.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164