Luguden Wutan Jirgin Sojoji Ya Halaka Babban Kwamandan Yan Ta'adda, Alhaji Modu

Luguden Wutan Jirgin Sojoji Ya Halaka Babban Kwamandan Yan Ta'adda, Alhaji Modu

  • Luguden wutan jirgin yaƙin sojojin sama NAF ya halaka babban kwamandan yan ta'adda, Alhaji Modu, da mayaƙa 50 a arewa maso gabas
  • Hedkwatar tsaro ta ƙasa ta bayyana cewa dakarun soji na cigaba da ruwan wuta ba kakkauta wa kan mafakar yan ta'adda a yankin
  • A wurin taron mako bibbiyu, DHQ ta sanar da cewa yan ta'adda 1755 tare da iyalansu ne suka ji uwar bari suka miƙa wuya ga sojoji

Abuja - Hedkwatar tsaro (DHQ) ta bayyana cewa a cigaba da ruwan bama-baman da ake wa yan ta'adda, babban kwamandan ƙungiyar ta'addanci ISWAP, Alhaji Modu (Aka Bem Bem) da wasu mayaƙa 50 sun sheƙa barzahu.

Ƙasurgumin ɗan ta'addan, wanda ke cikin jerin yan ta'addan da sojoji ke nema ruwa a jallo ya mutu ne a wani samamen sama na sojojin Operation Haɗin Kai a Degbawa kusa da Dutsen Mandara, ƙarmar hukumar Gwoza, jihar Borno.

Kara karanta wannan

2023: Makusancin Ministan Buhari Ya Koma PDP Yayin da Wani Gwamnan Adawa Ya Kulla Ƙawance da APC

Jirgin Sojojin Saman Najeriya.
Luguden Wutan Jirgin Sojoji Ya Halaka Babban Kwamandan Yan Ta'adda, Alhaji Modu Hoto: @Thenationnews
Asali: Twitter

Daraktan yaɗa labarai na DHQ, Manjo Janar Benard Onyeuko, shi ne ya bayyana haka a wurin taron da ake shirya wa bayan mako biyu da manema labaran hedkwatar a Abuja, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Ya ƙara da cewa gwarazan Sojojin Najeriya sun shirya kakkaɓe baki ɗaya wuraren da yan ta'adda ke mafaka da su.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yan ta'adda sun miƙa wuya

Ya ce adadin yan ta'adda 1755 tare da iyalansu da suka ji uwar bari ne suka miƙa wuya ga dakarun soji a tsawon wannan lokacin biyo bayan ruwan wutan sojoji ba kakkauta wa.

Punch ta ruwaito a jawabinsa ya ce:

"Rundunar Operation Haɗin Kai bata yi ƙasa a guiwa ba wajen kokarin mamaye baki ɗaya yankin da ke ƙarƙashinta yayin da take gudanar da ayyukanta a kauyuka, duwatsu, garuruwa da birane."

Kara karanta wannan

Kokarin Ɗinke Barakar PDP Ya Gamu da Cikas, Shugabar Mata da Daruruwan Mambobi Sun Koma APC

"Mazajen sojoji sun yi wa mayakan Boko Haram/ISWAP kwantan ɓauna a kan hanyar Uzoro-Gadamayo, jihar Adamawa, yayin artabu suka sheƙa ɗan ta'adda ɗaya, sauran suka tsere. Sun kwato bindigu kala daban-daban da alburusai."
"Haka nan tsakanin 27 ga Yuli zuwa 2 ga Agusta, Sojoji sun gudanar da sintiri, mamaya, shara da kai samame kan hanyoyin da suka haɗa Pulka-Shave axis, Gabachari, ƙauyen Doksa da Buni Yadi a jihohin Borno da Yobe."

A wani labarin kuma Ɓarayi Sun Kutsa Gidan Gwamnatin Katsina, Sun Yi Awon Gaba da Kuɗi Sama da Miliyan N30m

Wannan shi ne karo na biyu da aka yi irin wannan aika-aika ta sata a gidan gwamnati, wanda ya kamata ya kasance gini mafi tsaro a faɗin jihar.

A shekarar 2020, An sace makudan kuɗi da suka kai miliyan N16m a ofishin Sakatarem gwamnatin Katsina (SSG).

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262