Jerin Jihohin Biyar 5 Da Yara Ba Su Da Yanci A Najeriya
- Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ta ce jihohi 5 a Najeriya ba su kafa dokar kare hakkin yara ba
- Kungiyar UNICEF ta ce tana aiki tukuru wajen kai wa yara kanana marasa gata agaji a fadin duniya
- Kungiyar UNICEF tana aiki a wurare mafi wahala a duniya don kaiwa yaran dake fama da talauci a duniya agaji
Asusun lamunin kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ta ce kawo yanzu jihohi 5 cikin 31 na Najeriya ba su kafa dokar kare hakkin kananan yara ba.
Kungiyar kare hakkin yara ta kasa da kasa ce ta bayyana hakan a lokacin da ta yabawa gwamnatin jihar Kebbi bisa kafa dokar kare hakkin yara da ta yi kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito.
Kungiyar ta ci gaba da cewa UNICEF tana aiki tukuru wajen kai wa yara mara sa gata agaji a fadin duniya.
Ga Jerin Jihohin Da Unicef Ta Lissafo
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zamfara
Kungiyar UNICEF tana aiki a wurare mafi wahala a duniya don taimakawa yaran dake fama da talauci a duniya.
Unicef ta ce cikin Kasashe da yankuna fiye 190, suna shiga ko’ina kai agaji, suna son kowani yaro ya samu ingantacciyar rayuwa a duniya
Wani Dan Kasuwar Kasar Saudiya Ya Mutu Yana Tsaka Da Jawabi A Wani Faifan Bidiyo Mai Ban Tsoro
A wani labari kuma, Masar - Wani faifan bidiyo mai ban tsoro ya dauki lokacin da wani dan kasuwa ya fadi ya mutu a lokacin da yake jawabi a wani taro a Masar. Rahoton 21Centurychronicle
Rahotanni sun bayyana cewa, Muhammad Al-Qahtani, wani dan kasuwa daga kasar Saudiyya da ke zaune a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, ya yanke jiki ya fadi a lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen taron kasashen Larabawa da Afirka da aka yi a birnin Alkahira a ranar Litinin din da ta gabata.
Asali: Legit.ng