Ka Cika Ka Biya Albashin Ma'aikata: Malamin Addini Ya Ki Karbar Kyautan Miliyoyin Naira Da Gwamnan APC Ya Masa

Ka Cika Ka Biya Albashin Ma'aikata: Malamin Addini Ya Ki Karbar Kyautan Miliyoyin Naira Da Gwamnan APC Ya Masa

  • Bishop John Ebele Ayah, na cocin Katolika a Jihar Cross Rivers ya yi wani abin mamaki da ya burge mutane a wurin taro
  • Yayin bikin ban godiya don karrama mai shari'ar Emmanuel Agim Akomaye, Bishop Ayah ya mayarwa Gwamna Ben Ayade kyautan N25m da ya masa
  • Malamin addinin nan ta ke a bainar jama'a ya karbi na'urar magana ya fada wa Gwamna Ayade ya yi ciko a kudin ya biya albashin ma'aikata a jihar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Cross Rivers - Malamin Addini Ya Ki Karbar Kyautan Zunzurutun Kudi Da Gwamnan APC Ya Masa, Ya Ce Ya Tafi Ya Biya Albashin Ma'aikata Da Kudin, rahoton The Sun.

Wani abu mai kama da dirama ya faru a wani cocin katolika a Jihar Cross Rivers inda wani wani malamin addini, Bishop John Ebele Ayah, bishop na Uyo, ya ki karbar kyautan kudi daga hannun Gwamna Ben Ayade.

Kara karanta wannan

Atiku v Wike: Barakar Cikin PDP Ta Yi Zurfi, Jam’iyya Ta Gagara Yin Muhimmin Taro

Gwamna Ayade Da Bishop Ayah
Ka Yi Ciko Ka Biya Albashin Ma'aikata: Malamin Addini Ya Ki Karbar Miliyoyin Naira Da Gwamnan APC Ya Bashi. Hoto: (Photo: Cardinal Ekandem Seminary, @senatorbenayade).
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Lamarin ya faru ne a yayin addu'o'in ban godiya a cocin St. Patrick a Ikot Ansa, Jihar Calabar don karrama Mai Shari'a Emmanuel Agim Akomaye wanda aka masa karin girma zuwa kotun koli, Business Day ta rahoto.

Gwamna Ayade ya bada tallafin Naira Miliyan 25 ga cocin a madadin iyalansa da gwamnatin jihar a wurin taron da Ayah ya jagoranta.

Amma bayan ya sanar da bada tallafin, Ayah, ya juya ya cewa Ayade, ya ce:

"Abin alfaharinmu, abin alfaharin Cross River ta Arewa, dan mu, Bishop John Ayah, zan aika masa da sako na anjima."

Amma, cikin martanin gaggawa, Bishop ya karbi na'urar magana ya fada wa gwamnan ya dauki kudin, ya kara wani abu a kai ya biya albashin ma'aikata,' hakan yasa mahalarta taron suka fara ihu suna jinjinawa Bishop din suna cewa, 'Gangariyar Bishop, Allah ya maka albarka!".

Kara karanta wannan

Yajin Aikin ASUU: Ba Dole Ne Sai Kowa Ya Yi Digiri Ba, In Ji Gwamnan APC

Kalamansa:

"Ina son yin magana. Gwamna dan uwa na ne. Dukkan mu daga Cross River North muka fito. Ina son in gode wa gwamnan kuma in fada masa duk sakon da zai turo min, ya kara a kai, ya yi amfani da shi ya biya albashin ma'aikata."

Da ya lura da abin kunyan, gwamnan ya mayar da martani da cewa kudin biyan albashin ma'aikata yana nan daban kuma gwamnatinsa tana biyan albashi tsawo shekaru bakwai.

An ambato Ayade ya ce:
"Tuni an ware albashin ma'aikata. Ina son bayyana cewa gwamnatin nan na biyan albashi tun shekaru bakwai da suka wuce. Mutane za su gode wa Ben Ayade bayan ya bar ofis."

Laifin Tinubu Ne "Idan Amaechi Ya Koma PDP", Babban Jigon APC Ya Fasa Kwai

A wani rahoton, Chukwuemeka Eze, fitaccen jagora a jam'iyyar APC kuma na hannun daman Rotimi Amaechi, tsohon ministan sufuri, ya ce a dora wa Bola Tinubu laifi idan Amaechi ya bar jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Yadda Dan Najeriya Ya Badda Kamanni A Matsayin Mace A Facebook, Ya Damfari Dan Indiya Naira Miliyan 31

Eze yana magana ne kan wani rahoto da ke ikirarin cewa dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar yana zawarcin Amaechi, The Punch ta rahoto.

Idan za a iya tunawa Eze a baya-bayan nan ya kasance yana magana kan Amaechi kuma ya ce idan Amaechi ya shiga PDP, laifin Tinubu ne, wato dan takarar shugaban kasa na APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164