EFCC Za Ta Daure Mutum 2 da Suka Ci Kudi Saboda yi wa Tsofaffin Barayi Afuwa

EFCC Za Ta Daure Mutum 2 da Suka Ci Kudi Saboda yi wa Tsofaffin Barayi Afuwa

  • Akwai ma’aikata da ake zargi an yi amfani da su domin taba sunayen wadanda za ayi wa afuwa
  • Sunan Francis Atuche ya shiga cikin mutane 162 da Gwamnati ta nema a fito da su daga kurkuku
  • Daga baya aka fahimci ‘yan kwamitin PACOM aka biya kudi, suka bada sunan shi ta bayan fage

AbujaPremium Times tace hukumar EFCC ta na zargin wasu mutum biyu a ma’aikatar shari’a ta kasa da karbar cin hanci da nufin yafewa Francis Atuche.

Ana tuhumar wadannan ma’aikata da laifin karbar kudi domin a cusa Francis Atuche wanda tsohon ma’aikacin banki ne cikin jerin mutanen da za ayi wa afuwa.

Ma’aikatan sun yi aiki ne a karkashin kwamtin shugaban kasa na PACPM wanda ke zakulo tsofaffin marasa gaskiya wanda gwamnati za ta yafe masu laifinsu.

Kara karanta wannan

Yadda Dan Najeriya Ya Badda Kamanni A Matsayin Mace A Facebook, Ya Damfari Dan Indiya Naira Miliyan 31

Majiyar jaridar tace wadanda ake zargi da laifin karbar cin hancin su ne Emmanuel Fan wanda ya rike sakataren kwamitin PACOM tare da Lawrence Marinus.

An dauko dukkanin jami’an ne daga ma’aikatar shari’a ta tarayya domin su yi aiki da kwamitin. A karshe aka zarge su da karbar cin hanci domin ayi aika-aika.

Punch ta rahoto cewa akwai na ukunsu wanda ake zargin ya bada cin hancin kudi a madadin Mista Atuche, yanzu haka hukumar EFCC tana neman sa ido rufe.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Muhammadu Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a Aso Villa Hoto: BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

Kwamitin PACOM mai mutum 12

Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya ne ya jagoranci aikin wannan kwamiti mai mutum 12, ya gabatar da sunayen mutane 162 da ke daure.

Jerin da aka mikawa shugaban kasa ne aka gabatar a wajen taron majalisar koli na kasa a watan Afrilu, aka kuma samu amincewarsu wajen yi wasunsu afuwa.

Kara karanta wannan

2023: Abubuwa 5 da za su taimakawa Peter Obi a kan Tinubu, Atiku da Kwankwaso

Atuche ya shiga cikin sunaye 162

Daga cikin mutum 162 da aka kawo, majalisar kolin tayi fatali da sunayen wasu uku. Francis Atuche yana cikin wadanda ba a yarda a yafe masu laifin da suka yi ba.

Atuche yana gidan kurkuku bisa zargin satar Naira biliyan 27 daga bankin PHB wanda ya ruguje. A Yunin 2021 aka daure shi, ana sa ran zai yi shekaru shida.

Rahoton yace an nemi a yafewa Atuche saboda uzurin rashin lafiya, amma ba ayi na’am da hakan ba. Bayan nan sai AGF ya koka da cewa an taba jerin sunayen.

Ana zargin da za a kai sunayen wajen shugaban kasa ne sai Emmanuel Fan ya hada-kai da Marinus, aka hada da sunan Atuche. Amma jam'in ya karyata zargin.

Atuche bai wuce shekara a daure ba

A baya an rahoto cewa Francis Atuche wanda ya sace Naira biliyan 25 daga banki, ya shiga sahun wadanda Muhammadu Buhari ya nemi ayi wa afuwa a kurkuku.

Tun lokacin aka ji hukumar EFCC na binciken mukarraban Ministan shari'a, Abubakar Malami SAN a kan wannan batu da ya jawowa kasar abin kunya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng