Abia, Benue da Wasu Jihohi 13 da Suka Gaza Aiwatar da Tsarin Albashin N30,000 Ga Malamai
- Majalai a Najeriya, musamman na Firamare na daga cikin ma'aikatan da ke samun kudade mafi kankanta a matsayin albashi
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarun baya ya sanya hannu kan dokar karin kudin albashi da akalla kada ya gaza N30,000
- Sai dai, shin kowace jiha ce ta dauki wannan batu na Buhari, mun kawi muku jerin jihohin da suka fara biya, da kuma wadanda suka gaza
Najeriya - Shekaru uku bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan dokar kara albashi zuwa mafi karanci a kasar nan, har yanzu malaman makarantun firamare da sakandare na wasu jihohi 15 ba su fara cin gajiyar karin albashin na N30,000 ba.
Kungiyar malamai ta Najeriya (NUT) ce ta bayyana hakan, inji wani rahoton da jaridar The Nation ta fitar a makon nan.
Jihohin dai su ne kamar haka:
- Abia
- Bayelsa
- Delta
- Enugu
- Nasarawa
- Adamawa
- Gombe
- Nijar
- Borno
- Sokoto
- Anambara
- Imo
- Benue
- Taraba
- Zamfara
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Jihohi 15 ne kadai a Najeriya ke aiwatar da mafi karancin albashi na N30,000, inji NUT
Bayanai daga kungiyar ta malamai sun nuna cewa jahohi 15 ne kadai suka aiwatar da tsarin albashin malaman firamare da na sakandire kamar yadda Buhari ya sanya hannu, ciki har da babban birnin tarayya Abuja.
Ga dai jerinsu kamar haka:
- Akwa Ibom
- Ebonyi
- Edo
- Ekiti
- Jigawa
- Kano
- Katsina
- Kwara
- Legas
- Ogun
- Ondo
- Osun
- Oyo
- Plateau
- Rivers
- FCT
Hakazalika, akwai kuma jihohin ke tsaka-tsaki a tsarin, irinsu Kogi, Cross River, Kaduna da Yobe suna biyan mafi karancin N18,000 na 2011.
A watan Afrilun 2019 ne shugaba Buhari ya rattaba hannu a kan dokar mafi karancin albashi na N30,000 bayan shan fama da kungiyoyin kwadago.
Gwamna Zulum Ya Tabbatar Wasu Malamai Na Karban Albashi Kasa da N11,000 a Wata
A wani labarin, gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ya tabbatar da cewa akwai wasu Malamai na matakin kananan hukumomi, LEA da ke karɓan albashin N11,000 duk wata ko ƙasa da haka.
A wata sanarwa da gwamnan ya fitar a shafinsa na Twitter, Zulum ya ce baki ɗaya Malaman Sakandire da ke faɗin jihar na karɓan Albashi dai-dai da ƙunshin mafi karancin albashi N30,000.
Mai magana da yawun gwamnan, Malam Isa Gusau, ne ya yi wannan bayanin yayin da yake martani kan wasu Hotunan da ke yawo a kafafen sada zumunta, waɗan da ke nuna sakon Albashin wasu Malamai ƙasa da N10,000.
Asali: Legit.ng