Yan Bindiga Sun Gamu da Cikas Yayin da Suka Yi Yunkurin Garkuwa da Basarake a Kano

Yan Bindiga Sun Gamu da Cikas Yayin da Suka Yi Yunkurin Garkuwa da Basarake a Kano

  • Jami'an yan sanda da haɗin guiwar yan Banga sun fatattaki yan bindiga, sun kubutar da Basaraken da suka yi yunkurin sace wa a Kano
  • Kakakin yan Sandan Kano, Abdullahi Kiyawa, ya ce sun ceci Dagacin Garin Babba, kuma sun kwato Babura uku
  • Hakan na zuwa ne a dai-dai lokacin da Jirgin NAF ya sheƙe wani kasurgumin ɗan ta'adda da wasu 17 a Kaduna

Kano - Dakarun yan sanda da mambobin kungiyar yan banga sun daƙile yunkurin garkuwa da Dagacin Kauyen Garin Babba, da ke ƙaramar hukumar Garun Mallam, a jihar Kano.

Daily Trust ta rahoto cewa masu garkuwa sun farmaki kauyen Garin Babba da misalin ƙarfe 3:30 na dare wayewar garin Talata kuma suka yi awon gaba da Dagacin amma jami'an tsaro suka kwato shi.

Kara karanta wannan

Wasu Mutum Uku Sun Tsallake Rijiya da Baya a Hannun Mutane Bayan Asirin Su Ya Tonu a Abuja

Bajen hukumar yan sanda.
Yan Bindiga Sun Gamu da Cikas Yayin da Suka Yi Yunkurin Garkuwa da Basarake a Kano Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Kakakin hukumar yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce a ranar 9 ga watan Agusta, 2022 da karfe 1:30 na dare, sun samu rahoton wasu yan bindiga sun sace Dagacin.

Ya ce bayan samun rahoton, "Tawagar dakarun yan sanda na sashin yaƙi da masu garkuwa, jami'an ofishin yan sandan Garun Mallam bisa jagorancin DPO, CSP Usman Maisoro, da taimakon yan banga suka shirya domin ceto dagacin da cafke maharan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, masu garkuwan sun tsere suka bar Dagacin da Babura Uku, inda ya ƙara da cewa an samu nasarar kuɓutar da Basaraken babu ko kwarzane da kwato Babura uku.

Mun daƙile harin - Yan Banga

Jaridar Ripples Nigeria ta rahoto Wani mamban kwamitin tsaro a Garun Malam, Aminu Garba Ali, ya ce:

"Sum shigo da misalin ƙarfe 3:30 na dare kuma suka yi yunkurin tafiya da Magajin Gari, ba su iya tafiya da shi ba saboda Yan banga sun rufar musu, suka ceto Basaraken da Babura uku."

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Jirgin Sojojin NAF Ya Halaka Kasurgumin Ɗan Ta'adda, Alhaji Shanono, da Wasu 17 a Kaduna

A wani labarin kuma Jirgin Sojojin NAF Ya Halaka Kasurgumin Ɗan Ta'adda, Alhaji Shanono, da Wasu 17 a Kaduna

Hukumar Sojin Saman Najeriya NAF ta ce Jirginta ya halaka kasurgumin ɗan ta'adda, Alhaji Shanono, da wasu mayaka a Kaduna.

Jirgin ya kuma yi raga-raga da maboyar su da kayan aiki a kauyen Ukambo mai kilomita sama da 100 tsakaninsa da garin Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262