Yajin Aikin ASUU: Ba Dole Ne Sai Kowa Ya Yi Digiri Ba, In Ji Gwamnan APC

Yajin Aikin ASUU: Ba Dole Ne Sai Kowa Ya Yi Digiri Ba, In Ji Gwamnan APC

  • Gwamna Dave Umahi na Jihar Ebonyi ya ce ba wajibi bane kowa sai ya tafi jami'a a Najeriya ya samu kwalin digiri
  • Shugaban na kungiyoyin gwamnonin jihohin kudu maso gabas ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin tawagar asusun yan sandan Najeriya
  • Umahi ya ce akwai bukatar a yi garambawul ga tsarin ilimi a Najeriya domin karatu mafi karanci da kasashen duniya ke nema shina sakandare da karatun sana'o'i ba digiri ba

Gwamnan Jihar Ebonyi kuma shugaban kungiyar gwamnonin Kudu maso Gabas, David Umahi ya ce ilimin Jami'a fa ba na kowa da kowa bane, rahoton The Punch.

Umahi ya jadada cewa ba adalci bane a yi tsammanin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta ciyo bashin fiye da Naira tiriliyan 1 don biyan bukatun ASUU.

Kara karanta wannan

Duk Jamiyyar Da Taba Dan Arewa Damar Tsayawa Takarar Shugabankasa Bata Son Cigaban Najeriya - Akeredolu

Gwamna Umahi.
Yajin Aikin ASUU: Ba Dole Ne Sai Kowa Ya Yi Digiri Ba, In Ji Gwamnan APC. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya yi wannan jawabin ne kan yajin aikin da malaman jami'o'i ke yi, a lokacin da ya karbi bakuncin tawaga daga asusun yan sandan Najeriya karkashin jagorancin Dr Ben Akabueze, a Abakaliki a ranar Laraba.

Legit.ng ta rahoto cewa a baya-bayan nan ASUU ta tsawaita yajin aikin da aka shafe fiye da wata biyar ana yi.

Ilimin sakandare da na sana'a ne ginshiki da kasashe ke mayar da hankali a kai, Umahi

Gwamnan, wanda ya lura cewa ilimi da tsaro suna manyan kallubalen da ke adabar Najeriya, ya ce ba a tsara bangaren ilimin na Najeriya yadda ya dace ba, yana mai cewa ilimi mafi karanci da kowane kasa ke neman samu shine sakandare ko ilimin sana'o'i.

Umahi, ya ce a ranar Laraba:

"Matsalolin da suke ci mana tuwa a kwarya a kasar sune tsaro, kiwon lafiya da ilimi. Bari in ce a bangaren ilimi wanda shine ake fili wanda ASUU ke magana kai. Ina ganin ba a tsara bangaren ilimin mu yadda ya kamata ba.

Kara karanta wannan

Yadda Dan Najeriya Ya Badda Kamanni A Matsayin Mace A Facebook, Ya Damfari Dan Indiya Naira Miliyan 31

"Ilimin Jami'a ba na kowa da kowa bane kuma wannan shine gaskiya. Ilimi mafi karanci da kowanne kasa ke mayar da hankali kai shine sakandare da ilimin sana'a. Wannan sune jigo idan kana da su, za ka iya amfani da su ko ka fara wani abu ko a iya daukan ka aiki."

Ya cigaba da cewa:

"Akwai bukatar yiwa tsarin ilimin garambawul. Ba dole sai kowa ya yi ba. Bana jin kunyar fadi cewa digiri na ke da shi mataimaki na kuma yana da digirin digirgir; ba shine ke da muhimmanci ba. Abin da za ka iya yi shine. Don haka, Ban ga dalilin da zai sa ba zamu iya zama da shugabannin ASUU mu warware matsalar yajin aikin ba."

Gwamnan ya ce babu yadda Najeriya za ta iya ciyo bashin Naira tiriliyan daya amma dai za a iya fara biyan kudin kadan-kadan.

Yajin Aikin ASUU: Yanzu Dankali Na Ke Sayarwa, In Ji Lakcaran Jami'ar Najeriya

Kara karanta wannan

A Karshe, Buhari Ya Yi Magana Kan Abin Da Ya Janyo Yakin Basasa Na 1967, Ya Bayyana Mafita Ga Najeriya

A wani rahoton kun ji cewa Christiana Pam, wata lakcara a Jami'ar Uyo, Jihar Akwa Ibom, ta ce sana'ar sayar da dankali ta runguma domin kula da kanta tun bayan fara yajin aikin ASUU.

A ranar 14 ga watan Fabrairu ne ASUU ta fara yajin aikin gargadi na sati hudu. Kungiyar ta tsawaita yajin aikin da watanni biyu a ranar 14 ga watan Maris don bawa gwamnati daman biya musu bukatunsu. Ta sake tsawaitawa da sati 12 a ranar 9 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164