Shugaba Buhari Ya Naɗa Habiba Lawal a Matsayin Mai Bashi Shawara

Shugaba Buhari Ya Naɗa Habiba Lawal a Matsayin Mai Bashi Shawara

  • Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya naɗa Dokta Habiba Lawal, a matsayin mai bashi shawara ta musamman
  • Habiba Lawal ta taɓa rike mukamin sakatariyar gwamnatin tarayya ta riko a shekarar 2017
  • Malam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban ya ce tuni Dakta Lawan ta kama aiki a sabon ofishinta

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya naɗa Dakta Habiba Lawal, a matsayin mai ba shi shawara ta musanna kan tsari da daidaito.

Channesl TV ta ruwaiyo cewa naɗin na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasan, Malam Garba Shehu, ya fitar ranar Laraba.

Dr. Habiba Lawal.
Shugaba Buhari Ya Naɗa Habiba Lawal a Matsayin Mai Bashi Shawara Hoto: @channesltv
Asali: Twitter

A cewar Sanarwan, "Kafin ta yi ritaya, Dakta Lawal ta cimma nasara yayin jagorantar tawagar tsare-tsare, bincike da aiwatar da ayyukan magance kalubalen muhalli a sassan ƙasar nan tare da sakamako abun yabo."

Kara karanta wannan

Tikitin Musulmi-Musulmi: Paparoma bai ce na yi kuskuren marawa Tinubu da Shettima baya ba, inji Lalong

"Ta yi karatun digirinta na farko a jam'ar Ahmadu Bello da ke Zariya daga 1982-1986 a fannin BSc Chemistry. A nan ne ta lashe lambar yabon Ɗaliba mafi hazaka a aji biyu na Kamfanin Tobacco a shekarar 1984/1985."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Haka nan ta lashe lambar yabon ɗalibar da ta kammala karatu da sakamako mai kyau a Kwas dinta, sannan kuma ta lashe lambar yabon dalibar da ta yi aikin nazari mafi kyau duk a shekarar 1985/1986."
"A 1991, Habiba ta samu shaidar gama karatun Digiri na biyu daga jami'ar ABU Zariya. Daga nan ta wuce jami'ar fasaha da ke Bauchi ATBU inda ta yi karatun digiri na uku (PhD) kuma ta samu shaidar kwarewa daga wata jami'ar Birtaniya."

Wane muƙami ta taba rikewa a gwmanati?

Malam Shehu ya ƙara da cewa Dakta Habiba Lawal ta rike mukaddashin Sakatariyar gwamnatin tarayya daga 19 ga watan Afrilu, 2017 zuwa 30 ga watan Oktoba, 2017.

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: Yan Majalisar Dokokin Jihar Katsina Zasu Sa Labule da Gwamna da Shugaba Buhari

A wani labarin kuma Daga Ƙarshe, Shugaban APC na kasa ya Magantu Kan Shirin majalisa na tsige shugaba Buhari

Shugaban APC, Abdullahi Adamu, ya ce yunkurin yan majalisar tarayya na tsige Buhari wani cigaba ne abun takaici da nadama.

Tsohon gwamnan jihar Nsarawan ya ce haka na faruwa a kowace kasa amma har waɗan da suka kirkiri lamarin sun gudu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262