Yadda Dan Najeriya Ya Badda Kamanni A Matsayin Mace A Facebook, Ya Damfari Dan Indiya Naira Miliyan 31

Yadda Dan Najeriya Ya Badda Kamanni A Matsayin Mace A Facebook, Ya Damfari Dan Indiya Naira Miliyan 31

  • Wani matashi dan Najeriya ya shiga hannu a kasar Indiya inda ake zarginsa da damfarar wani mutum kudi har naira miliyan 31
  • Dan Najeriyan ya badda kamanni a matsayin mace bayan ya bude shafin bogi a Facebook
  • Yana ta turawa mutane sakon kulla kawance kuma da zaran sun amince sai ya nemi aika masu da sakon kaya, a nan ne yake damfararsu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Rundunar yan sanda a kasar Indiya ta kama wani dan Najeriya kan damfarar wani mutum kudi har naira miliyan 31 bayan ya kama soyayya da shi a Facebook.

Yan sanda a ranar Juma’a, 10 ga watan Agusta, sun ce an kama wanda ake zargin mai suna Oliver, a Humayunpur karkashin ofishin yan sandan Saffarjang da ke Delhi.

Babban jami’in dan sandan sashin Uttarakhand STF, Ajai Singh ya bayyana cewa an dauko wanda ake zargin zuwa Uttarakhand, shafin LIB ya rahoto.

Kara karanta wannan

Hotuna: Tsantsar Kyawun Wani Ango Da Amaryarsa Ya Sa Mutane Yamutsa Gashin Baki A Soshiyal Midiya

Dan Najeriya a Indiya
Yadda Dan Najeriya Ya Badda Kamanni A Matsayin Mace A Facebook, Ya Damfari Dan Indiya Naira Miliyan 31 Hoto: LIB
Asali: UGC

A cewarsa, da yiwuwar dan Najeriyan da abokan aikinsa sun damfari mutane daga sauran jihohin ma.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Singh ya ce akwai yiwuwar sake kama wasu mutane da ke da alaka da lamarin.

Ya kara da cewa:

“Wani mamba na kungiyar na iya barin kasar da nufin guduwa, don haka an tuntubi ofishin jakadanci.”

An samo na’urar laftof biyu, wayoyin hannu takwas, layukan waya bakwai, na’urar wi-fi hudu, na’urar tantance kati daya, katin memori uku, da sauransu daga hannun wanda ake zargi.

Yadda abun ya fara

Oliver ya bude wani shafin Facebook na bogi da sunan wata yar kasar waje sannan ya aikewa mutane sakon kulla abota.

Bayan sun yarda da abotan nashi, sai ya nemi aika masu da kyaututtuka na kulla abota.

Sai kuma ya sa su biyan kudi ta yanar gizo da sunan kudin sauke kaya na kwastam.

Kara karanta wannan

Ministoci Sun Samu Sabani a Taron FEC, Shugaban Kasa ya Raba Masu Gardama

Rundunar yan sandan ta kuma ce bayan ya damfarar su makudan kudade, sai ya goge shafin bogin da ya bude daga Facebook.

Wanda ya damfara a Uttarakhand mai suna Suresh Arya, wanda ya kasance mazaunin Ranikhet ya shigar da kara a sashin yan sanda masu yaki da laifukan yanar gizo, yankin Kumaon a Rudrapur, Lifestyle Nigeria ta rahoto.

Ma’aurata Sun Maka Makwabcinsu Da Zakaransa A Kotu, Hotunan Sun Yadu

A wani labarin, wani dattijon kasar Jamus, Friedrich-Wilhelm K. da matarsa, Jutta sun maka makwabcinsu a kotu saboda hayaniya.

Friedrich ya ce makwabcinsu na da wani zakara, Magda, wanda suka yi ikirarin cewa yana cara sau 200 a rana; lamarin da suka bayyana a matsayin ‘azabtarwa’.

Ma’auratan sun fara shirye-shiryen kai mai Magda, Michael, gaban kotun yankin kan caran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng