Arzikin Aliko Dangote ya ragu zuwa dala biliyan 19, wanda yanzu ya zama na 80 mafi arziki a duniya

Arzikin Aliko Dangote ya ragu zuwa dala biliyan 19, wanda yanzu ya zama na 80 mafi arziki a duniya

  • Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote, ya dawo kasa daga cikin jerin manyan attajiran duniya
  • Dangote ya haura zuwa Attajirin Duniya na 60 a watan Yuni kafin ya fado gab da ya shiga jerin attajirai duniya guda 50
  • Akwai kadarorin Dangote Masu Daraja da ba saka su a cikin kiddidgar fitar da sunayen attajiran duniya saboda ba su fara aiki ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Legas - Aliko Dangote, wanda ya kafa kamfanin Dangote kuma attajirin da ya fi kowa kudi a Nahiyan Afirka, ya ga an daidaita kiyasin dukiyarsa yayin da ake sayar da hannun jari a Simintin Dangote. Rahoton Legit.NG

A lokacin da aka kammala zaman ciniki na ranar Talata, arzikin dan kasuwar dan asalin jihar Kano ya dawo dala biliyan $19, wanda ya mayar da shi 80 a cikin jerin attajiran duniya da kididdigar Bloomberg ta fitar.

Kara karanta wannan

Ministoci Sun Samu Sabani a Taron FEC, Shugaban Kasa ya Raba Masu Gardama

A cewar kididdigar Bloomberg, wacce ta fitar da sunayen attajiran duniya 500, yanzu dukiyar sa ta ragu zuwa dala biliyan 19 sabanin dala biliyan 20 a watan Mayun 2022.

Dangote
Arzikin Aliko Dangote ya ragu zuwa dala biliyan 19, wanda yanzu ya zama na 80 mafi arziki a duniya FOTO Legit.NG
Asali: UGC

Adadin arzikin da Dangote yake da shi a halin yanzu ya sa ya zama mutum na 80 a cikin attajirai a duniya, daga na 60 a cikin watanni biyu kacal da suka wuce.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farashin da aka yi a kasuwar hada-hadar hannayen jarin Najeriya na baya bayan nan ya nuna cewa Dangote Cement ya rufe kasuwa akan N241.00 a ko wani kaso, inda ya ragu da kashi 9.06 cikin dari, inda ya yi ciniki kusan mako 52 da ya yi kasa da Naira 237, lamarin da ya sa attajirin yayi asarar dala miliyan 863 a kullum.

Mafi akasarin arzikin Dangote ya fito ne daga mallakar kashi 86% na simintin Dangote, wanda ake sayar da shi a bainar jama'a. Kai tsaye da kuma ta hannun kamfaninsa na Dangote Industries, ya mallaki hannun jari a kamfanin kamar yadda nairametrics.com ta rawaito.

Kara karanta wannan

Lauje cikin nadi: Majalisa za ta titsiye ministar kudi kan batun kudaden tallafin man fetur

Sai dai Kamfanin taki wanda shine mafi daraja a cikin kadarorinsa da matatar mai da ake ginawa a Najeriyana na dala biliyan 19 ba sa cikin dukiyoyin sa da Bloomberg ta sanya a cikin kiddidigar fitar da jerin sunayen attajiran duniya.

Yan Takara Biyar Da Suke Kan gaba Wajen Neman Kujerar Masari

A wani labari kuma, Jihar Katsina - Yan takarar gwamna 13 ne suka fito takara a zaben badi a jihar Katsina, bayan zaben fidda gwani na jam’iyyun siyasa daban-daban. Amma, biyar ne kawai daga cikinsu ake ganin za su yi fice a zaben. Rahoton The Nation

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta fitar da jerin sunayen jam’iyyun siyasa 13 da ‘yan takararsu na zaben gwamna a jihar Katsina mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa