A Karshe, Buhari Ya Yi Magana Kan Abin Da Ya Janyo Yakin Basasa Na 1967, Ya Bayyana Mafita Ga Najeriya
- An gargadi yan Najeriya daga kowanne bangare kan su guji daukan wani mataki da zai jefa kasar cikin wani yakin basasa
- Shugaba Muhammadu Buhari ne ya yi wannan kirar yayin ziyarar da tsaffin shugabanni jihohi na tsohuwar jam'iyyar CPC suka kai masa
- Shugaban kasar ya ce dole shugabanni su cigaba da aiki don ganin Najeriya ta cigaba da zama kasa daya dunkulalliya
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
FCT Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Talata ya ce gwamnatinsa za ta cigaba da ganin cewa Najeriya ta cigaba a matsayin kasa daya, The Punch ta rahoto.
Da ya ke tuna baya kan abubuwan da suka faru a lokacin yakin basasa na 1967-1970, shugaban kasar ya ce an yi sadaukarwar tabbatar da hadin kan Najeriya. Don haka dole shugabannin siyasa su cigaba da daukan matakan tabbatar da hadin kan kasa.
A cewar wata sanarwa mai dauke da sa hannun mashawarcin shugaban kasa na musamman kan kafafen watsa labarai, Femi Adesina, Buhari ya furta hakan ne yayin da ya karbi bakuncin tsaffin ciyamomi na tsohuwar jam'iyyar CPC na jihohi a villa a Abuja.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Taken sanarwar, 'Mu yan Najeriya ne, Da izinin Allah za mu cigaba da zama yan Najeriya, kuma Najeriya za ta cigaba da zama daya, in ji Shugaba Buhari.'
Son kai ya janyo yakin basasar 1967 - Buhari
Shugaban kasar ya ce ba za a bari son kai da ya janyo rasa rayyuka kimanin miliyan daya a 1967 - 1970 ya sake faruwa ba.
Ya ce:
"Babban abin da muka sa a gaba shine tarayyar Najeriya. Mu yan Adam ne. Muna da nakasu, amma ina tabbatar muku cewa kishin kasar da muke da shi ba da sauki muka same shi ba. Kun san abin da na ke nufi da wannan, mun kashe mutum miliyan cikinmu don tabbatar da cewa kasar nan bata rabu ba.
"Ba na tunanin akwai wata darasi na zahiri da ya fi wannan. Mu yan Najeriya ne , Da izinin Allah za mu cigaba da zama yan Najeriya, kuma Najeriya za ta cigaba da zama daya".
Shugaban kasar ya kuma yi jinjina ga tsaffin ciyamomin na tsohuwar jam'iyyar CPC yana mai cewa ya na farin ciki da ziyarar da suka kawo masa domin za su tattauna wasu batutuwa na cigaban kasa.
Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Ya Koka Kan Tsadar Rayuwa, A Yayin Da Farashin Kaya Ke Cigaba da Tashi A Kasar
A wani rahoton, tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya Olusegun Obasanjo a ranar Talata 2 ga watan Agusta ya shiga jerin miliyoyin yan Najariya da ke kokawa kan tsadar rayuwa da wasu abubuwan.
Obasanjo ya bayyana cewa yana keta gumi sosai saboda tsadar dizal wanda ke shafar kasuwancinsa da wasu kasuwancin a sassan kasar.
Daily Trust ta rahoto cewa tsohon shugaban kasar ya yi wannan jawabin ne a wurin taron masu kiwon kifi na kudu maso yamma da aka yi a dakin karatu na Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo (OOPL) a Abeokuta, Jihar Ogun.
Asali: Legit.ng