Gwamna Wike na Ribas: Ko da Kun Cire Ni a PDP Zan Tsinana Abin Alheri Ga Jama’a
- Gwamna Wike na jihar Ribas ya bayyana irin abubuwan da ya sa a gaba, ya ce shugabanci nagari ba daga jam'iyyara yake ba
- A yau ne gwamna Wike ya gayyaci jigon siyasar APC domin kaddamar da wasu ayyuka a jihar Ribas
- Ana ci gaba da musayar maganganu tsakanin gwamna Wike na Ribas da dan takarar shugaban kasa na PDP
Jihar Ribas - Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya ce ingantaccen shugabanci nagari bai da alaka kuma bai shafi jam’iyyun siyasa ba, Daily Trust ta ruwaito.
Wike ya bayyana haka ne a wajen bikin kaddamar da titin Ogbunuabali-Eastern Bypass wadda wani jigon jam’iyyar APC Sanata Aliyu Wamakko ya halarta a jiharsa a ranar Talata.
Gwamnan ya ce ba daidai ba ne mutane su yi tunanin cewa shugabanci aiki ne na jam’iyyun siyasa, yana mai cewa aiki ya shafi tunani ne na mutum.
“Shugabanci ba na jam’iyya bane, shugabanci na mutum ne, Jam’iyya tsani ce kawai don aiwatar da burin ku, don samun damar gaya wa mutanenku ina da wannan ƙarfin, Ina da wannan ingancin da zan yi muku."
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wike ya bayyana cewa kauna, sha'awar sa da jajircewarsa na yi wa mutanen Ribashidima mai inganci sun bambanta shi da sauran 'yan siyasa, inji Vanguard.
Shi ya sa, in ji shi, akwai ci gaba da himma wajen kara kima ga rayuwa, tasiri ga sauyi tare da karfin hali na samar da ababen more rayuwa da inganta jihar a ransa.
Sanata Wammako: Wike yana da kishin yiwa al'ummarsa hidima
Wike ya ce yayin da wasu suka yi amfani da matsalar tattalin arziki a matsayin uzuri don kin yiwa jama’arsu hidima, ya sami wata hanya mai kyau don yiwa 'yan Ribas ayyuka ma su ma'ana.
Da yake kaddamar da titin Ogbunuabali –Eastern Bypass, tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, ya ce Wike ya nuna cewa yana da kishin yiwa al’ummar Ribas hidima.
Sanata Wamakko ya ce ya kamata duk wata gwamnati mai ma’ana ta yi aiki don biyan bukatu da buri na al'umma. Ya lura cewa a matsayinsa na gwamna, Wike ya yi wa jama’arsa kyakkyawan aiki.
PDP Ta Dage Taronta Na NEC da Majalissar Wakilai Yayin da Rikicin Tsakanin Atiku da Wike Ke Kara Ruruwa
A wani labarin, jam’iyyar PDP ta dage taronta na kwamitin zartarwa na kasa (NEC) da ‘yan majalisar wakilai na kasa, biyo bayan dambarwar da ta dade tsakanin dan takararta na shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ke kara dagulewa.
A tun da farko dai an shirya gudanar da tarukan gabobi biyu masu muhimmancin ne a gobe Laraba da kuma Alhamis, rahoton The Guardian.
Tinubu na kawai karfe 4 na dare bai yi barci ba yana aiki saboda tsananin kwazonsa , Shugaban matasan APC Dayo Isarel
Wata sanarwa da sakataren jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Samuel Anyanwu, ya fitar, ta ce an dage zaman ne saboda wasu abubuwan da suka bullo da ba a yi tsammani ba.
Asali: Legit.ng