WASSCE 2022: Yadda Za A Duba Sakamakon WAEC Ta Sakon Tes Da Intanet
Legas, Najeriya - A ranar Litinin, 8 ga watan Agusta, Hukumar Shirya Jarrabawa ta WAEC ta fitar da sakamakon jarrabawar daliban 2022 na babban ajin karshe na sakandare wato WASSCE.
Sakamakon, a cewar shugaban ofishin hukumar na kasa, Patrick Areghan, an fitar da shi ne kwana 45 bayan rubuta jarrabawa ta karshe.
Ga Daliban da suka rubuta jarrabawar, a wannan rahoton za a nuna hanyoyi biyu da za su iya tuba sakamakon jarrabawarsu: Sakon tes da kuma shafin yanar gizo
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kafin fara duba sakamakon, ana bukatar katin duba jarrabawar. Ana bukatar lambar pin da serial number da ke cikin katin don duba sakamakon.
Yadda za a duba sakamon WAEC ta hanyar sakon tes
1. Da wayar salula, Rubuta WAEC*LambarJarrabawa*PIN*ShekararJarrabawa
2. Aika sakon zuwa ga 32327
3. Nan take za ka samu sako dauke da sakamakon ka na jarrabawar WAEC
Abin Lura: Masu amfani da layukan MTN, Glo da Airtel ne kadai za su iya amfani da wannan tsarin na sakon tes. Idan ba turo sakamakon ba, a sake maimaita tura sakon.
Kazalika, za a caje kudin tura sakon na tes yayin duba sakamakon WAEC ta hanyar SMS.
Akwai bukatar a siya katin duba jarrabawa wato Scratch Card kafin duba jarrabawar ta hanyar tes.
Yadda za a duba sakamakon jarrabawar WAEC ta shafin yanar gizo na WAEC
A ziyarci shafin www.waecdirect.org kuma a shiga
Abin Lura: Ana bukatar katin WAEC don duba sakamakon, sai a bi matakan da ke kasa.
1. Shiga shafin duba jarrabawar WAEC a shafin yanar gizo: www.waecdirect.org
2. Shigar da lambar jarrabawa
3. Zabi irin jarrabawa, misali, May/June
Da zafi-zafi: Sojoji sun gano dan ta'addan da ya kitsa kai hari kan tawagar Buhari a Daura, sun sheke shi
4. Zabi shekarar da aka rubuta jarrabawa misali 2022
5. Latsa 'Check Result'.
Yadda za a duba ta hanyar Serial Number
1. Da farko, a tabbatar akwai intanet a wayar salular
2. A ziyarci shafin www.waecdirect.org
3. Shigar da lambar jarrabawa mai dauke da lambobi 10
4. Shigar da Serial Number
5. Shigar da shekarar jarrabawa kuma
6. Latsa 'Check my WAEC Result'.
Asali: Legit.ng