Gwamnatin Katsina Ta Maida Yan Gudun Hijura 12,000 Gidajen Su, Ta Ware Miliyoyi
- Gwamnatin jihar Katsina ta ware makudan kuɗaɗe ta maida yan gudun hijira 12,000 gidajen su a kauyen Shinfida, karamar hukumar Jibiya
- Gabanin maida su gida, gwamna Aminu Masari ya tattauna da shugaba Buhari kuma ya tabbatar da za'a tura sojoji
- A ranar 10 ga watan Maris, mazauna kauyen suka bar gidanjen bayan ɗauke sojoji daga yankin
Katsina - A ranar Litinin, gwamnatin Katsina karkashin jagorancin gwamna Aminu Bello Masari, ta maida yan gudun hijira sama da 12,000 da suka haɗa da mata da yara zuwa gidajen su a ƙauyen Shimfiɗa, ƙaramar hukumar Jibiya.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa yan gudun Hijirar sun koma ƙauyen su ne bisa rakiyar tsattsauran matakan tsaro.
Mutanen sun bar muhallan su ne ranar 10 ga watan Maris biyo bayan ɗauke dakarun soji daga yankin wanda ya haddasa ƙaruwar hare-haren yan fashin daji wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.
Gabanin komawar su gida, sama da yan gudun Hijira 6,000 gwamnatin jiha da ta yankin suka jibge a Makarantar Sakandiren yan mata (GGSS) Jibiya, yayin da wasu suka tsere zuwa wasu yankunan Jamhuriyar Nijar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wane mataki gwamnatin ta ɗauka don gyara musu rayuwarsu?
Shugaban ƙaramar hukumar Jibiya, Bishir Sabi’u, ya ce tuni gwamnatin Katsina ta saki miliyan N88.6m domin maida mutanen gida.
A cewarsa, hakan ya biyo bayan wata miliyan N18m da gwamna Aminu Masari ya ware domin samar musu da magunguna a Asibiti, kayayyakin rayuwa ga mutanen, da ma'aikata.
Ya ce gabanin maida yan gudun hijiran gida, gwamna Masari ya tattauna da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, kuma ya tabbatar masa da za'a samar da tsaro.
A ruwayar Channels tv, Bishir Sabiu ya ce:
"Dalilin mu na dawo da su gida shi ne wasu sun fara noma a gonakin su na yankin, don haka muna son su koma sana'ar su ta noma gadan-gadan."
"Tashin Sojoji a yankin ya jawo tarwatsewar su kuma gwamna ya yi magana da Buhari, tuni an amince da sake jibge sojoji."
Da yake jawabi, shugaban ƙungiyar matasan cigaba na Shimfiɗa, Sa'ad Salisu, ya nuna gamsuwarsa da matakin shirin da gwamnati ta yi na maida yan gudun hijiran gida.
Ɗan majalisa mai wakiltar Katsina a majalisar dokokin tarayya, Aliyu Abubakar, ya ce shi da takwarorinsa sun shirya gana wa da Masari daga bisani su gana da Buhari domin lalubo hanyar warware matsalar tsaron da ta addabi jihar.
A wani labarin kuma Jam'iyyar APC ta faɗi sunan wani gwamnan PDP da idan ya zarce a 2023 matsalar tsaro zata ƙara Lalacewa
Jam'iyyar APC a jihar Oyo ta yi gargaɗin cewa tsaron jihar na cikin matsala idan har gwamna Makinde ya zarce a Ofis a 2023.
A wata sanarwa, APC mai adawa a jihar ta ce daga zuwan Makinde ya lalata duk wani tubalin zaman lafiya da tsohon gwamna ya gina.
Asali: Legit.ng