Yarinya 'Yar Shekara 22 Dauke Da Juna Biyu Ta Ce Tana Son Masoyinta Mai Shekaru 88

Yarinya 'Yar Shekara 22 Dauke Da Juna Biyu Ta Ce Tana Son Masoyinta Mai Shekaru 88

  • Wata Matashiya mai 22 shekaru ta ce zuciyarta ta kamu da son wani mutum mai suna Kasher Alphonse wanda ya isa ya zama kakanta mai shekaru 88
  • Alphonse ya auri matarsa ta farko a shekara ta 1954 a lokacin yana dan shekara 24 wanda suka haifi ’ya’ya bakwai tare
  • Baban Dan Kasher Alphonse yana da shekaru 66 da haihuwa yayin dan autan sa yana da shekaru 50

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Chibalonza tana da shekaru 22, amma zuciyarta ta kamu da son wani mutum mai suna Kasher Alphonse wanda ya isa ya zama kakanta mai shekaru 88. Rahoton Legit.NG

Masoyan sun shafe shekaru biyu suna tare da juna, inda suka ce zukatan su ke soyayya, ba shekarun su ba.

Alphonse ya auri matarsa ta farko a shekara ta 1954 a lokacin yana ɗan shekara 24 wanda suka haifa ’ya’ya bakwai tare.

Kara karanta wannan

Mafi tsufa a raye: An gano wani tsoho dan Najeriya mai shekaru 126 a raye kuma da karfinsa

Bayan shekaru da yawa suna tare, matarsa ta farko ta mutu saboda tsufa, ta bar dattijon cikin kadaici yayin da 'ya'yansa suka girma suka bar gida.

Duk da yawan shekarunsa, Alphonse yana da ƙoƙarin ya yi wa kansa yawancin komai, don haka ya nemi wacce zata taimaka masa da abun da yake bukata.

Alphonse
Yarinya 'Yar Shekara 22 Dauke Da Juna Biyu Ta Ce Tana Son Masoyinta Mai Shekaru 88 FOTO Afrimax Media
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi sa'ar haduwa da Chibalonza, wanda ta kasance yar shekara 20 wanda a shirye take zama matarsa.

Yace ba su yi aure a hukumance ba amma anyi bikin auren gargajiya da ita, har ma na kai wa ‘yan uwanta akwatunan giya da akuya mai rai inji Alponse.

Dattijom ya bayyana cewa bai san yadda ‘ya’yansa za su yi mu’amala da matar sa ba idan ya mutu, amma bai damu da hakan ba.

Abin baƙin cikin sa shi ne, ba shi da kuɗin siyan fili da zai gina wa karamar matarsa gida don ta samu mafaka bayan ran sa.

Kara karanta wannan

Wani Dan Najeriya Ya Fashe Da Kuka Yayin Da Budurwar Sa Ta Nemi Auren Sa Da Kyautar Tsaleliyar Mota

Chibalonza wanda take da juna biyu a yanzu tana sa ran Alphonse yana shirin gudanar da bikin auren su. Mutane da yawa suna matukar mamaki soyayyar su saboda duka ’ya’yan Alphonse sun girmi matar sa, yayin da babban dansa yana da shekaru 66 autan sa yana da shekaru 50.

Alphonse wanda ya kanjame kuma talauci ya nuna a jikin sa, ya ce yana samun kuɗi sosai a zamaninsa kuma ya mallaki kantin sayar da giya. Sai dai kuma kasuwancin ya rufe ne bayan wasu ‘yan fashi da suka addabe shi yasa jarin sa suka kare.

Ka Nuna Wa Yan Ta’adda Kaine ke Mulkin Najeriya – Afenifre Ga Buhari

A wani labari kuma, Gamayyar Kungiyar Yarabawa ta Afenifere, ta roki shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya nuna cewa har yanzu shi ne ke jagorantar kasar. Rahoton Daily Trust

Yayin da kungiyar ke bayyana damuwarta kan matsalar rashin tsaro a Najeriya, kungiyar ta yi mamakin ko Buhari na sane da halin da kasar ke ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel