Ka Nuna Wa Yan Ta’adda Kaine ke Mulkin Najeriya – Afenifre Ga Buhari

Ka Nuna Wa Yan Ta’adda Kaine ke Mulkin Najeriya – Afenifre Ga Buhari

  • Gamayyar Kungiyar Yarabawa ta Afenifere, ta roki shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya nuna cewa har yanzu shi ne ke jagorantar kasar
  • Kungiyar Afenifere ta ce rikon sakainar kashi da gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro suke wa harka tsaro a kasar yasa yan ta'adda suka kara karfi
  • Afenifere ta ce abun takaici ne ganin yadda yan ta'adda suke kaima hukumomin jami'an tsaro hari yadda suka ga dama

Gamayyar Kungiyar Yarabawa ta Afenifere, ta roki shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya nuna cewa har yanzu shi ne ke jagorantar kasar. Rahoton Daily Trust

Yayin da kungiyar ke bayyana damuwarta kan matsalar rashin tsaro a Najeriya, kungiyar ta yi mamakin ko Buhari na sane da halin da kasar ke ciki.

Sakataren Yada Labarai na kungiyar Afenefere, Kwamared Jare Ajayi, da yake karin haske game da kashe-kashe da kuma sace-sacen mutane don neman kudin fansa a fadin kasar nan ya ce babu wani yanki na kasar da ke da tsaro.

Kara karanta wannan

2023: Ku kwantar da hankali, za a yi zaben 2023 ba tare da wata matsala ba, hafsan tsaro

Buhari
Ka Nuna Wa Yan Ta’adda Kaine Mulkin Najeriya – Afenifre Ga Buhari Legit.NG
Asali: UGC

Ya bayyana cewa a Ogbomoso da ke jihar Oyo a yankin Kudu-maso-Yamma, an samu rahotannin sace mutane uku tare da kashe su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ajayi ya kara da cewa rashin tsaro ya tabarbare ne saboda yadda ake yiwa harkar tsaro rikon sakainar kashi a kasar.

Yan ta’adda da masu garkuwa da mutane sun kara karfi, ta yadda a yanzu suna iya kai farmaki ga hukumomin tsaro yadda suka ga dama, kuma ba abun da zai faru, duk a karkashin kulawar gwamnati da hukumomin tsaro kamar yadda jaridar THIS DAY ta rawaito.

Rashin tsaro ya kai ga yan ta’adda sun shiga gida bayan gida suna ta’adi kuma babu mai taka musu birki.

Kamar wani hari da suka kai karamar hukumar Bali ta Jihar Taraba a ranar 7 ga watan Augusta Inda suka kashe mutane uku tare da yin garkuwa da mutane da ba san adadin su ba inji Ajayi.

Kara karanta wannan

Da zafi-zafi: Sojoji sun gano dan ta'addan da ya kitsa kai hari kan tawagar Buhari a Daura, sun sheke shi

Ajayi ya bayyana cewa dole ne kalaman shugaban kasa ya wuce yin Allah wadai ya tabbatar wa ‘yan ta’addan cewa har yanzu shine ke rike da madafun iko a kasar.

'Yan Bindiga Sun Kashe Rayuka Uku, Sun Sace Mutane da Dama a jihar Taraba

A wani labari kuma, Wasu yan bindiga sun kai hari garin Bali, hedkwatar ƙaramar hukumar Bali a jihar Taraba, inda suka kashe mutum uku kuma suka sace wasu da dama ranar Lahadi da daddare.

Wasu majiyoyi da yawa a Bali sun shaida wa wakilin Punch cewa yan bindigan sun farmaki jami'ai a shingen bincike da ke kusa da babban Asibitin garin, daga bisani suka hari mutane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel