'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Surukar Sanata Mai Wakiltar Katsina Ta Arewa

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Surukar Sanata Mai Wakiltar Katsina Ta Arewa

  • Yan bindiga sun yi awon gaba da mutum huɗu a Kankia, jihar Katsina cikin su har da matar ƙanin Sanata Ahmed Babba Kaita
  • Sanata Kaita na wakiltar shiyyar Katsina ta arewa a majalisar dattawan Najeriya, yankin da shugaba Buhari ya fito
  • Wasu masu garkuwa sun kashe direban wata Mota a hanyar Funtua saboda yaki yarda ya bi su

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Katsina - Yan bindiga sun yi awon gaba da mutum hudu cikin su har da surukar Sanata mai wakiltar mazaɓar Katsina ta arewa a majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Babba Kaita.

Daily Trust ta rahoto cewa Daura, garin da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya fito na ƙarƙaashin shiyyar Katsina ta arewa.

Wani mazaunin Kankia, Muhammad Sani, ya ce maharan sun farmaki garin ne a farkon awannin yau Litinin kuma suka ci karen su babu babbaka na tsawon awanni.

Kara karanta wannan

Daga Ƙarshe, Shugaban APC Na Ƙasa Ya Magantu Kan Shirin Majalisa Na Tsige Shugaba Buhari

Taswirar jihar Katsina.
'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Surukar Sanata Mai Wakiltar Katsina Ta Arewa Hoto: punchng
Asali: UGC

Ya ce faramakin ya faru ne a Anguwar Bakin Kasuwa, inda yan bindigan suka kutsa kai gidan Mani Babba Kaita, ƙanin Sanata Ahmed Babba Kaita, suka yi awon gaba da matarsa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ƙara da cewa maharan sun kuma shiga gidan wani Sabe Halilu a wannan Anguwa, inda suka ci zarafin matarsa kana suka sace ƴaƴansa biyu, cikin su har da ɗalibar Firamare.

Wani mazaunin Kankia na daban, Salisu Musa, ya ce maharan sun sace wata matar aure duk a wannan Anguwa ta Bakin Kasuwa.

Mutumin ya ce:

"Gaskiya sun zo ne da nufin sace ɗan uwan Sanatan, amma ya fice daga gidan. Ɗaya daga cikin matansa ta tsira, amma wacce abun ya shafa ta ga ba zata iya guduwa ta bar ƴaƴanta ba, shiyasa suka same ta."
"Ɗayar matar kuma mijinta baya nan lokacin da suka zo, yayin da ta yi nufin guduwa sai maharan sun cafko ta suka lakaɗa mata duka, suka haɗa da 'ya'ya biyu. A baki ɗaya harin, sun sace matan aure biyu da kananan yara biyu."

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: 'Yan Shi'a 6 da Jami'an Tsaro Suka Bindige a Zaria

Kankiya wani gari ne da ke kan hanyar Katsina zuwa Kano kuma wannan ba shi ne karo na farko da yan bindiga suka kai farmaki garin ba, kamar yadda Channels ta ruwato.

Yadda lamarin ya faru

Wani mazaunin garin Kankia ya faɗa wa wakilin Legit.ng Hausa cewa maharan sun shigo da karfe 1:30 kuma da nufin shiga gidaje biyu, Usman Babba Kaita (Mani) da wani ma'aikacin hukumar shige da fice da ake kira Sabe Halilu.

Mutumin wanda ya nemi a ɓoye sunansa ya shaida wa wakilin mu cewa:

"A gidan Mani Babba Kaita, (watau Kanin sanata) sun ɗauki uwar gidansa, Hajiya Mairo Mani. Sai kuma suka kutsa gidan Sabe suka ɗauki matarsa da farko amma Allah ya taimaketa ta gudu."
"Sai suka koma gidan suka ɗakko yarsa Amira, da wani yayanta da bazan iya tuna sunansa ba. Akwai wani ɗan Bijilanti da tsautsayi yasa ya faɗa musu suka masa harbi uku, yanzu haka yana Asibiti."

Kara karanta wannan

El-Rufai Ya Sace Gwiwan Kakakin Atiku, Ya Ce Ko Gawarsa Ba Za A Tsinta Kusa Da PDP Ba

Mutumin ya kara da sun ci karen su babu babbaka domin babu wani jami'in tsaro da ya kawo ɗauki tsawon lokaci sai wannan ɗan Bijilanti da suka harba.

A wani labarin kuma Yadda ma'aikata masu ɗaukar albashi a Najeriya suka koma tafiyar kafa saboda tsadar Kuɗin Mota

Farashin kudin tafiye-tafiya a motar haya na ƙara tashi biyo bayan ƙarin farashin Litar Fetur a Najeriya.

Wasu masu ɗibar Albashi sun fara maye gurbin shiga motar Bas zuwa wurin aiki da tafiyar kafa domin rage kuɗi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262