Shugaba Buhari Ya Nada Tsohon Dan Majalisar Kano a Matsayin Hadiminsa

Shugaba Buhari Ya Nada Tsohon Dan Majalisar Kano a Matsayin Hadiminsa

  • Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya naɗa tsohon ɗan majalisar tarayya, Nasiru Ila, a matayin mai taimaka masa kan harkokin majalisa
  • Mista Ila zai hau kujerar da Umar El-Yaƙub ya bari bayan shugaban ya naɗa shi Minista a baya-bayan nan
  • Naɗin na zuwa ne a lokacin da shugaban ke fuskantar barazanar tsige wa daga majalisar wakilai nan da makonni

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya naɗa Nasiru Ila, a matsayin babban mai taimaka masa ta fannin harkokin da suka shafi majalisar tarayya (Majalisar wakilai), kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

A wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasa, Malam Garba Shehu, ya fitar ranar Lahadi, Mista Ila zai maye gurbin da Umar El-Yaƙub ya bari, wanda aka naɗa muƙamin Minista a baya-bayan nan.

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Shugaba Buhari Ya Nada Tsohon Dan Majalisar Kano a Matsayin Hadiminsa Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Honorabul Ila ya zauna a kujerar ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Tarauni a majalisar dokokin tarayya daga shekarar 2011 zuwa 2015. Kuma ya yi karatunsa a makarantun Birtaniya.

Kara karanta wannan

Rikicin Cikin Gida: Bayan Shan Kaye, Ɗan Uwan Shugaba Buhari Ya Fice Daga Jam'iyyar APC

Babban ƙalubalen da ke gaban sabon hadimin

Sabon hadimin shugaban ƙasan ya zo ne a dai-dai lokaci mai cike da ƙalubale kasancewar shugaban na fuskantar barazanar tsige wa daga wasu yan majalisun tarayya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jim kaɗan gabanin tafiyar mambobin majalisar hutu, yan Majalisun tsagin hamayya sun ba shugaba Buhari wa'adi ya shawo kan matsalar tsaron da ta addabi Najeriya.

A cewarsu, matukar shugaban ya gaza cika sharadin a wa'adin da suka ɗibar masa, zasu fara bin matakan tunbuke shi daga kan kujerar shugaban ƙasa.

Wasu mambobin majalisun tarayya da ke cikin jam'iyyar All Progressive Congress APC, sun nuna goyon bayan tsige Buhari duk da suna jam'iyya ɗaya.

A wani labarin kuma kun ji cewa NAHCON ta kammala kwaso Alhazan Najeriya daga kasa mai Tsarki, ta yi magana kan matsalolin da aka samu

Kara karanta wannan

Sanatoci Na Shirin Tsige Shi, Wata Jam'iyyar Adawa Ta Goyi Bayan Kira Ga Shugaba Buhari Ya Yi Murabus

Hukumar jin daɗin Alhazai ta ƙasa NAHCON ta kammala dukkan ayyukan aikin Hajjin 2022 bayan jirgin karshe ya baro Jiddah.

Shugaban Hukumar, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan, ya amince da matsalolin da aka samu da kuma matakin da zasu ɗauka a gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262