'Yan Ta'adda Sun Sheka Barzahu Yayin Wani Artabu da Sojoji A Jihar Borno

'Yan Ta'adda Sun Sheka Barzahu Yayin Wani Artabu da Sojoji A Jihar Borno

  • Yan ta'addan ISWAP sun gamu da ajalin su yayin da suka yi yunkurin kai hari sau biyu garin Monguno da ke jihar Borno
  • Wani jami'in hukumar tattara bayanan sirri ya ce da yawan yan ta'addan sun sheƙa barzahu a musayar wuta da sojoji na awanni
  • A cewar wasu bayanai maharan sun yi yunkurin ɗaukar fansa bayan harin farko, amma sai suka sake kwasar kashin su a hannu

Borno - Mazajen Sojojin Najeriya sun yi nasarar daƙile harin wasu da ake zargim mayaƙan ƙungiyar ta'addanci ISWAP ne a garon Monguno, jihar Borno, arewa maso gabashin Najeriya.

The Cable ta tattaro cewa yan ta'addan sun shiga garin ne da misalin ƙarfe 8:30 na dare ranar Jummu'a tare da motocin yaƙi, Babura da muggan makamai, suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Birnin Katsina, Sun Halaka Rai Sun Sace Ma'aurata

Sojojin Najeriya.
'Yan Ta'adda Sun Sheka Barzahu Yayin Wani Artabu da Sojoji A Jihar Borno Hoto: vanguard
Asali: Depositphotos

Wani jami'in hukumar tattara bayanan sirri ya shaida wa Zagazola Makama, masani kuma mai sharhi kan harkokin tada ƙayar baya cewa Sojoji sun tarbi yan ta'addan, suka yi musayar wuta har karfe 11:30 na dare.

Rahoto ya nuna cewa a wannan artabu da dakarun sojin Najeriya ne da yawan yan ta'adda suka sheƙa barzahu, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Majiyar ta ƙara da cewa Dakarun sojin sun dakile wani hari makamancin wannan duk a garin Monguno ranar Alhamis da karfe 2:00 na wayewar gari lokacin da yan ta'addan suka yi yunkuri kai wa soji hari a Abbari Kasuwan Shani.

Ya ce sojojin, waɗan da suka samu labarin motsin zuwan yan ta'addan, sun tarbe su, suka yi kazamin artabu inda suka kashe yan ta'adda Shida, wasu da dama suka tsere da raunin harsashi. Soja ɗaya ya rasa rayuwarsa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Wani Babban Malami A Najeriya

Harin ɗaukar fansa

Jami'in sashin haɗa bayanan sirrin ya ce bayan haka ne ISWAP ta haɗa mayaƙanta a Babura 12 da motocin yaƙi Shida suka taso daga Marte da Kukawa da nufin zuwa ɗaukar fansa.

Ya ce yunkurin yan ta'addan ya gamu da mazajen fama inda dakarun soji na Operation Haɗin Kai suka sheƙe da yawan su, wasu suka tsere bisa tilas.

A wani labarin kuma kun ji cewa 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Wani Babban Malami A Najeriya

Wasu tsageru sun je har gida sun sace wani babban Malamin addinin kirista a yankin ƙaramar hukumar Orumba ta arewa, jihar Anambra.

Wasu bayanai da aka tattara sun nuna cewa maharan sun ɗauke malamin ne da tsakar dare bayan ya kammala addu'o'i.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262