1999 Zuwa 2022: ASUU Ta Bata Akalla Shekaru 7 da Sunan Yajin Aiki
Yawan shiga yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ke yi na tilasta wa daliban Najeriya zama a gida tare da bata lokaci mai tsada na karatu, kuma hakan ya faro ne tun daga shekarar 1999.
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Matakin da kungiyar ta ASUU ke dauka a lokuta da dama sakamakon gazawar gwamnati wajen biyan wasu bukatunta, kan kawo cikas ga dalibai da dama, lamarin da ke haifar da tasgaro a fannin ilimi tare da karya gwiwar daliban ga romon ilimi.
Tun daga gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo zuwa gwamnatin Buhari, bayanai sun nuna cewa kimanin zangon karau 15 (wato shekaru bakwai) aka yi asararsu da sunan yajin aikin ASUU.
A kasa, Legit.ng Hausa ta kawo muku cikakken jerin lokutan da dalibai suka yi nesa da azuzuwa sakamakon yajin malamansu na ASUU:
Dubu Ta Cika: Jami'an NDLEA Sun Kama Wani Soja Mai Ritaya Ɗan Shekara 90 Dake Kaiwa Yan Bindiga Kwayoyi
Mulkin Obasanjo (1999-2007 PDP)
A mulkin Obansajo kadai dalibai sun yi asarar watanni 18 da kwanaki 3 da sunan yajin aiki, sakamakon gazawar gwamnati wajen biyan bukatar ASUU.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duba jerin lokutan:
- 1999: Watanni 5
- 2000: - Watanni 3
- 2002: - Makonni 2
- 2003: - Watanni 6
- 2005: - Makonni 2
- 2006: - Kwanaki 3
- 2007: - Watanni 3
Mulkin 'Yar Adua da Jonathan a hade (2008-2015 PDP)
Daga farin mulkin marigayi Umaru Musa 'Yar Adua har zuwa karshen mulkin shugaba Goodluck Ebele Jonathan, dalibai sun yi tagumin rashin zuwa makaranta sakamakon yajin ASUU na akalla watanni 16 da kwanaki 6.
Duba jerin lokutan:
- 2008: Mako 1
- 2009: Watanni 4
- 2010: Watanni 5
- 2011: Kwanaki 59
- 2013: Watanni 5
Mulkin manjo Muhammadu Buhari mai ritaya (2015-2022 APC)
A iya mulkin Manjo Muhammadu Buhari mai ritaya da har yanzu bai kare ba, an bata akalla watanni 29 kuma har yanzu ana kai.
Duba jerin lokutan:
- 2017: Wata 1
- 2018: Watanni 3
- 2020: watanni 9
- 2021: Watanni 11
- 2022: - Watanni 5
Yajin aikin ASUU: Dalibin aji 2 a jami'a ya koma sayar da shayi a Kano
A wani labarin, wani dalibin aji biyu na Jami’ar Yusuf Maitama Sule da yajin aiki ASUU ya shafa ya kama wata sana’ar sayar da “Shayi” a garin Dawakin Dakata da ke karamar hukumar Nassarawa ta jihar Kano domin kaucewa zaman banza.
Dalibin mai karanta Tarihi da Hulda da Kasashen Duniya wanda ya bayyana sunansa da Yusuf Auwal Barkum, a wata hira da ya yi da Sahelian Times, ya ce ya yi nadamar rashin kama sana’ar tun da farko.
Teburin shayi dai kasuwanci ne na gida inda ake sayar da dafaffiyar taliya, kwai, shayi da burodi, galibi a fili da ke da karamin shago da benci, teburi da kujeru a zagaye dasu.
Asali: Legit.ng