Kakakin PDP Bwala: Muna Nan Daku, El-Rufai Zai Lallaba Ya Koma Jam’iyyar PDP Nan Gaba
- An yi hasashen daya daga cikin manyan matsalolin da jam'iyyar APC za ta shaida nan ba da jimawa ba
- Hasashen da Bwala Daniel, mai magana da yawun yakin neman zaben Atiku Abubakar ya yi, ya hango makomar Gwamna Nasir El-Rufai ta siyasa
- Daniel a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a baya-bayan nan ya ce gwamnan na Kaduna zai koma jam’iyyar PDP kafin zaben 2023
Najeriya - Mai magana da yawun tawagar yakin neman zaben Atiku Abubakar, Bwala Daniel, ya yi hasashen abin da zai faru gabanin babban zaben 2023.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, 7 ga watan Agusta, Daniel wanda ya fice daga jam’iyyar APC a baya-bayan nan ya ce gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna zai koma jam’iyyar PDP nan ba da jimawa ba.
Jigon na PDP ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani kan batutuwa El-Rufai na matsayin zamansa a APC.
Daniel ya bayyana cewa ba zai yi jayayya da gwamnan ba saboda yana da kwarin gwiwa game da sauya shekarsa zuwa jam’iyyar adawa kafin 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya wallafa a Twitter cewa:
" An ja hankali ga batun @elrufai yana dariya kan wani tsokaci da aka yi a kaina akan faifan bidiyo na baya. Hmm.
"@elrufai yana daya daga cikin jiga-jigan da muke da su daga Arewa, ba zan taba jan daga da shi ba, musamman saboda ina da kwarin gwiwar cewa zai kasance tare da mu kafin zaben 2023."
Gwamna El-Rufai: Zan Tabbata a APC Daga Yanzu Har zuwa Mutuwa ta
Sai dai, gwamna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa yana daya daga cikin mutane 37 da suka daura tsintsiyar jam’iyyar APC tun farko don haka ya dauki jam’iyyar a matsayin daya daga cikin ‘ya’yansa, rahoton Leadership.
Gwamnan wanda ya bayyana hakan a wata tattaunawa ta kai tsaye a gidajen rediyon Kaduna a daren Laraba, ya karyata jita-jitar da ake yadawa na cewa yana shirin sauya sheka zuwa wata jam’iyya, kan batun Tinubu da Shettima.
El-Rufai ya sha alwashin ci gaba da kasancewa a jam’iyyar APC har zuwa karshen rayuwarsa, inda ya kara da cewa ‘’idan na bar APC, to na bar siyasa gaba daya’’.
Asali: Legit.ng