'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Birnin Katsina, Sun Halaka Rai Sun Sace Ma'aurata

'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Birnin Katsina, Sun Halaka Rai Sun Sace Ma'aurata

  • Wasu miyagun mutane dauke da bindigu sun kashe mutum ɗaya, sun bar wasu biyu da raunuka yayin harin da suka kai jihar Katsina
  • Harin na zuwa ne watanni biyu bayan sace mutum shida da yan bindiga suka yi a yankin ranar 14 ga watan Yuni
  • A kwanakin baya hukumomin tsaro a Najeriya sun bayyana cewa yan ta'adda na shirya kai hare-hare jihar Buhari

Katsina - A ranar Lahadin nan, wasu miyagun yan bindiga sun kashe aƙalla mutum ɗaya kuma suka jikkata wasu mutum biyu a wani hari da suka kai yankin gidajen Shola Quaters da ke cikin birnin Katsina.

Wannan harin ya zo ne watanni biyu bayan wasu yan ta'adda, ɗauke da muggan makamai, sun kai farmaki wannan yakin.

An kai sabon hari Katsina.
'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Birnin Katsina, Sun Halaka Rai Sun Sace Ma'aurata Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wani mazaunin yankin, wanda ya tabbatar da kai harin ga jaridar Channels TV ta wayar salula, ya ce 'yan bindigan sun shiga yankin a farkon awannin ranar Lahadi misalin ƙarfe 1:30.

Kara karanta wannan

Yan Ta'adda Sun Gamu Da Ajalinsu Hannun Sojoji Yayin Da Suka Yi Yunkurin Kai Kazamin Hari A Jihar Arewa

Ya ce maharan sun kuma sace wasu Ma'aurata a farmakin wanda ya shafe kusan mintuna 30 yan ta'addan na aikata mummunan nufin su.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mutumin ya ƙaraa da cewa tuni aka yi gaggawar kai waɗan da suka jikkata Asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya da ke kusa da yankin domin kula da lafiyar su.

Shola Quaters wani yanki ne da ke bayan babban Asibitin koyarwa na tarayya kuma yana fama da hare-hare ne saboda kusancinsa da maɓoyar yan bindiga da ke Bugaje, ƙaramar hukumar Jibiya.

A ranar 14 ga watan Yuni, wasu yan ta'adda suka sace mutum Shida yankin, amma ba su kashe kowa ba a harin, wanda suka kutsa kai gida-gida. Cikin waɗan da suka sace har da yarinya yar shekara biyu.

A wani labarin kuma kun ji cewa An kama kasurgumin Ɗan Ta'adda Da Hukumar yan sanda ke nema ruwa a jallo

Kara karanta wannan

Karin Bayani: An Kashe Yan Sanda 4, An Kona Motocci A Harin Da Yan Bindiga Suka Kai Caji Ofis

Dakarun yan sanda sun samu nasarar cafke wani ƙasurgumin ɗan kungiyar asiri da aka jima ana nema ruwa a jallo a jihar Osun.

Mutumin mai suna Rasheed Hammed, ya shiga hannu ne a maɓoyarsa da ke Osogbo, babban birnin jihar Osun yau Lahadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262