An Kama Kasurgumin Dan Kungiyar Asirin Da Yan Sanda Ke Nema Ruwa A Jallo A Osun

An Kama Kasurgumin Dan Kungiyar Asirin Da Yan Sanda Ke Nema Ruwa A Jallo A Osun

  • Dakarun yan sanda sun samu nasarar cafke wani ƙasurgumin ɗan kungiyar asiri da aka jima ana nema ruwa a jallo a jihar Osun
  • Mutumin mai suna Rasheed Hammed, ya shiga hannu ne a maɓoyarsa da ke Osogbo, babban birnin jihar Osun yau Lahadi
  • Tun a watan Maris, hukumar yan sanda ta ayyana nemansa bayan aikata wasu manyan laifukan kisan kai

Osun - Bayan watanni biyar da ayyana shi cikin jerin waɗan take nema ruwa a jallo, hukumar yan sanda reshen jihar Osun ta kama wani ƙasurgumin ɗan asiri, Rasheed Hammed.

Hammed wanda aka fi sani da Rasidi Oko’lu, ya jima cikin jerin waɗan da yan sanda ke nema bisa zargin ayyukan Asiri, ta'addanci, da sauran su.

Wata majiya mai ƙarfi ta shaida wa wakilin jaridar Punch cewa Oko’lu ya shiga hannun jami'an tsaro ne a maɓoyarsa da ke Osogbo, babban birnin jihar Osun.

Kara karanta wannan

Yan Ta'adda Sun Gamu Da Ajalinsu Hannun Sojoji Yayin Da Suka Yi Yunkurin Kai Kazamin Hari A Jihar Arewa

Kwamishinan yan sandan Osun, Olawale Olokode.
An Kama Kasurgumin Dan Kungiyar Asirin Da Yan Sanda Ke Nema Ruwa A Jallo A Osun Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Dakarun yan sanda na sashin yaƙi da muggan ayyukan Asiri ne suka je har inda ya ke ɓoye suka damƙo shi da misalin ƙarfe 4:00 na wayewar garin yau Lahadi, 7 ga watan Agusta, 2022.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun yaushe hukumar yan sanda ta ayyana nemansa?

Hukumar yan sandan Osun ta ayyana neman Oko’lu ruwa a jallo ne a watan Maris bayan ya aikata wasu manyaan ayyukan ta'addanci.

Bayanai sun nuna cewa wanda ake zargin ya yi sanadin mutuwar ɗalibin da ya kammala karatun babbar Diploma a fannin harkokin Banki da kuɗi daga makarantar kwalejin fasaha ta tarayya da ke Ede.

Kasurgumin ɗan asirin ya yi sanadin mutuwarsa ne yayin da yake jiran takardar kira domin fara aikin bautar ƙasa watau NYSC.

Haka zalika Oko'lu ya kashe wani ɗan Acaɓa, wanda ba'a bayyana cikakkun bayanansa ba yayin da suke faɗa a Ede.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Wani Babban Malami A Najeriya

Hukumar yan sanda ta tabbatar

Mai magana da yaawun hukumar yan sanda reshen jihar Osun, Yemisi Opalola, a wani sakon waya da ya aike wa wakilin jaridar Punch, ya ce, "Eh, mun kama shi a daren da ya gabata."

A wani labarin kuma Awanni Kaɗan Tsakani, Yan Bindiga Sun Sake Kai Wani Kazamin Hari Kusa Da Babban Birnin Jihar Katsina

Awanni kalilan a tsakani, yan bindiga sun sake kai hari wani ƙauye kusa da babban birnin jihar Katsina, jihar shugaban ƙasa.

Yan ta'addan sun kashe mutum uku, sun kuma yi awon gaba da gomman mutane mata da kananan yara a ƙauyen Dantsauni, yankin Batagarawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel