A Aljanna Ne Kawai Ba Za A Samu Matsalar Tsaro Ba, Yanzu Kuma Duniya Muke, Ministan Buhari, Keyamo
- Festus Keyamo, karamin ministan kwadago da ayyuka a Najeriya ya ce matsalar tsaro ba mizani ne da ke nuna FG ta gaza ba
- Keyamo ya ce gwamnatin tarayya bata yi alkawarin ba za a samu matsalar tsaro ba, ta yi alkawarin mayar da martani ne kuma tana yin hakan
- Ministan ya kara da cewa babu kasar duniya da ba a samun matsalar tsaro, yana mai cewa a aljanna ne kawai ba za a samu matsalar tsaron ba
Festus Keyamo, karamin ministan kwadago da samar da ayyuka, ya ce ba za a iya amfani da 'hare-haren' da aka kaiwa wasu sassan kasar ba a matsayin 'mizani' na cewa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta gaza.
Keyamo ya yi wannan jawabin ne a hirar da aka yi da shi a Channels Television a ranar Juma'a, The Cable ta rahoto.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cikin yan makonnin baya-bayan nan, munanan hare-hare sun karu a sassan kasar har da babban birnin tarayya, Abuja.
A watan Yuli, an kai hari gidan gyaran hali na Kuje a Abuja an kuma kashe wasu cikin jami'an tsaro masu gadin shugaban kasa.
Da ya ke magana kan lamarin, Keyamo ya ce gwamnatin Buhari bata yi alkawarin cewa ba za a samu hare-hare a kasar ba, ya kara da cewa kawai ta yi alkawarin za ta maida martani ne yadda ya dace.
"A makon da ta gabata, an kai wa wadanda ke taruwa a dazukan Abuja hari an fatattake su an kashe su," in ji shi.
"Wannan shine abin da muka yi alkawari, munyi alkawarin za mu mayar da martani. Ba mu yi alkawarin hari ba zai faru ba. Munyi alkawarin martani. Mun mayar da martani satin da ya gabata, mun kashe su.
Rashawar Da Aka Tafka a Gwamnatin Buhari Ta Fi Wanda Aka Yi Cikin Shekaru 16 Na Gwamnatin PDP, Tsohon Jigon APC, Bwala
"An samu tsaro a Abuja yanzu. Hakan bai sake faruwa ba a dazukan Abuja. Munyi alkawarin daukan mataki kuma munyi hakan.
"Mutane su dena firgita juna. Bari in fada maka wani abu game da yadda yan bindiga ke tunani. Tsorata mutane suke son yi. Tsoratarwa ne iskar da suke shaka. Suna son haifar da firgici. Shine iskar da yan ta'adda ke shaka.
"A aljanna ne kadai - idan mun tafi can ba za a samu hare-hare ba kwata-kwata. Ba mu shiga aljanna ba. Muna duniya ne, dole a samu hare-hare. Mun mayar da martani da ya dace.
"Ana kai hare-hare, ba haka muka so ba, amma ba mizani ne da za a ce gwamnati ta gaza ba. Ana kai hari gidan yari a Amurka. Wurin da ya fi tsaro a duniya, ana tserewa daga gidan yari.
"A kasashen yamma, ana kai hari gidan yari. Ba alfahari na ke da shi ba. Ba hujja na ke kafawa ba. Ina son gyara kalon da wasu yan Najeriya ke yi wa lamarin ne."
Dangi da 'yan uwa na saka 'yan siyasa satar kuɗin gwamnati, Ministan Buhari
A wani labarin daban, karamin ministan Kwadago da Samar da Ayyuka, Festus Keyamo SAN, ya ce matsin lamba da yan uwa da abokai ke yi wa mutane da ke rike da mulki ne neman su basu kudi ne ka karfafa musu gwiwa suna sata da aikata rashawa.
A cewar The Sun, Keyamo ya yi wannan furucin ne yayin jawabin da ya yi a ranar Laraba a Abuja yayin kaddamar da shirin 'Corruption Tori Season 2' da Signature TV da gidauniyar MacArthur suke daukan nauyi.
An kirkiri shirin ne domin wayar da kan mutane game da rawar da za su iya takawa wurin yaki da rashawa da cin hanci a Nigeria ta hanyar amfani da harsunan mutanen Nigeria.
Asali: Legit.ng