Ta'addanci: Kungiyar CAN Ta Kai Kuka Wurin Gwamnatin Amurka, Kungiyar Musulunci Ta MURIC Ta Yi Martani

Ta'addanci: Kungiyar CAN Ta Kai Kuka Wurin Gwamnatin Amurka, Kungiyar Musulunci Ta MURIC Ta Yi Martani

  • Kungiyar kare hakkin musulmi, MURIC, ta karyata ikirarin da kungiyar Kiristoci CAN ta yi na cewa kiristoci ne yan ta'adda suke kashewa kadai saboda addininsu
  • Farfesa Ishaq Akintola, shugaban MURIC ya ce hasali ma musulmi yan ta'addan suka fi kashewa domin hare-haren sun fi yawa a arewa kuma musulmi ke da rinjaye a arewan
  • Akintola ya ce kawai su al'ummar musulmi suna birne gawarwakinsu cikin gaggawa ne ko da yan ta'adda sun kai musu hari amma kiristoci na ajiye gawa na kwanaki ko watanni kuma suna nuna gawar a wurin jana'iza a yi ta daukan hotuna

Jihar Legas - Kungiyar kare hakkin musulmi ta MURIC ta dage cewar ikirarin da shugabannin kirista ke yi na cewa kiristoci kadai ake kashewa a Najeriya ba gaskiya bane, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

EFCC Ta Gayyaci Hadimar Ministan Buhari Kan Sayar Da Kadarorin Gwamnati Da Aka Kwato Daga 'Barayin Gwamnatin'

Farfesa Akintola
Ta'addanci: Musulmi Suka Fi Shan Wahala, MURIC Ta Yi Martani Ga Sanatocin Amurka. Hoto: @daily_trust.
Asali: UGC

Hakan martani ne kan sanarwar da sanatocin Amurka biyar, Josh Hawley, Marco Rubio, Mike Braun, James Inhofe da Tom Cotton wanda suka tura wa sakataren Amurka wasika mai kwanan watan ranar 29 ga watan Yunin 2022 suna ikirarin cewa "nuna cewa mutum kirista ne tamkar hukuncin kisa ne a sassan Najeriya da dama."

Sanatocin na Amurka sun fitar da sanarwar ne bayan takardar korafi da shugaban kungiyar kiristoci na Najeriya, CAN, ta rubuta na zargin cewa ana musgunawa kirista a kasar.

Martanin MURIC

A yayin jawabin wurin taron manema labarai a ranar Alhamis a Legas, shugaban MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya ce an fi kashe musulmi tun farkon ta'addancin a Najeriya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce a yayin da sanatocin na Amurka suka yi ikirarin cewa an kashe kirista 4000 a Najeriya zuwa shekarar 2021, duk da cewa yana tantama kan alkalluman, Akintola ya ce sunyi watsi da fiye da musulmi 40000 da aka kashe a wannan lokacin.

Kara karanta wannan

Ba za ta sabu ba: Kungiyar kiristoci ta fara yaki da ci da addini, za ta ba da katin shaida ga malamai

A cewar Ishaq, shugabannin kiristocin kawai suna amfani da kallubalen tsaro da kasar ke fama da shi ne a yanzu.

"Gaskiya shine kashi 90 cikin 100 na wadanda Boko Haram da ISWAP suka kaiwa hari musulmi ne tunda sun fi kai hare-hare a Arewa inda galibi musulmi.
"Don haka, musulmi ne wadanda rikicin ya fi shafa a Najeriya. Babu wani alkallami da zai canja hakar koda daga ina ya fito," in ji shi.
Ya cigaba da cewa ana ganin kamar an fi kashe kirista ne domin irin yadda suke birne gawarsu, "kiristoci a Najeriya suna nuna gawarwarki har suna jinkirta jana'iza da kwanaki ko watanni amma musulmi na birne nasu nan take ne ba tare da zuzuta abin ba. Dabara ce ta kyamara."

Shugaban na MURIC ya ce karya ne ikirarin da suke yi cewa gwamnatin Najeriya bata kare hakkin mutane su yi addinin da suke so.

A Zurfafa Bincike Kan Yaran Musulmi 21 Da Aka Ceto a Cocin ECWA Plateau, In Ji MURIC

Kara karanta wannan

2023: Kungiyar Kirista Ta Watsa Wa CAN Kasa A Ido, Ta Ce Ba Laifi Bane Tinubu Ya Zabi Mataimaki Musulmi

A wani rahoton, kungiyar Kare Hakkin Musulmi, MURIC, ta bukaci Sufeta Janar Na Yan Sanda, IGP, da Hukumar Yan Sandan Farin Kaya, DSS, ta bincike yadda aka gano tare da ceto yara musulmi 21 a wani gini mallakar cocin ECWA a Jos, Jihar Plateau.

Shugaban MURIC na kasa, Farfesa Ishaq Akintola ne ya yi wannan jiran cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Ya bayyana cewa a baya-bayan nan ne DSS ta kai samame wani gida da ke JMDB quaters a unguwar Tudun Wada a karamar hukumar Jos ta Arewa, inda jami'an suka ceto yaran musulmi 21.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164