A Dena Kawo Addini Cikin Siyasa, In Ji Lalong, Shugaban Yakin Neman Zaben Tinubu
- Simon Lalong, shugaban kungiyar yakin neman zaben Tinubu/Shettima a 2023 ya shawarci yan Najeriya su dena kawo addini cikin siyasa
- Gwamnan na Jihar Plateau ya ce ba addini bane ya kawo kallubalen da ake fama da shi a Najeriya don haka a mayar da hankali wurin karfafa zumunci da kawo cigaba
- Jigon na APC ya kuma ce tallata Tinubu/Shettima ba sabon abu bane domin ko a shekarar 2015 wasu sun ce ba zai ci zabe ba saboda ya shiga jam'iyyar musulmi amma kuma ya ci zaben
Gwamnan Plateau kuma shugaban kungiyar yakin neman zaben Tinubu/Shettima, Simon Lalong, ya bukaci yan Najeriya su dena kawo addini cikin siyasa su rungumi cigaba yana mai cewa ba addini ne ya haifar da kallubalen da ake fama da su a kasar ba yanzu, rahoton Nigerian Tribune.
Lalong, wanda ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da ya ke yi wa dandazon mutane jawabi a filin tashin jirage na Yakubu Gowon, Heipang a Jos, Jihar Plateau, ya yi alkawarin zai yi aiki tukuru don nasarar APC a zaben shugaban kasa na 2023.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A kan tikitin musulmi da musulmi, Lalong ya ce: "Yi wa Tinubu/Shettima kamfen ba zai zama sabon abu ba a Jihar Plateau. Irin wannan abin muka fuskanta a 2015 lokacin da wasu mutane suka ce ba za mu ci zabe saboda muna jam'iyyar musulmi ne amma mun ci zaben.
"Abin da nake so shine mu kara karfafa zumunci. Najeriya daya ne. Kallubalen da muke da shi ba daga musulmi ko kirista bane, kallubale daya ne kuma nauyin da ke kanmu shine hada kan mutane domin samun cigaba."
A dena saka addini a cikin siyasa, Lalong
Ya shawarci yan Najeriya su dena saka addini a siyasa su rungumi cigaba, ya kara da cewa kallubalen da ake fama da shi a kasar ba addini bane ya haifar da shi.
Gwamna Lalong ya ce nadin da aka masa matsayin shugaban kamfen din ya nuna cewa ana dama wa da mutanen Plateau a siyasar Najeriya kuma jihar za ta fidda APC kunya.
Lalong: Abin Da Yasa Ba Zan Goyi Bayan Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Daga Arewa Ba a APC
A baya, Simon Lalong, ya ce yana goyon bayan Rotimi Amaechi, tsohon ministan sufuri kuma dan takarar shugaban kasa na 2023, ya kuma ce ba zai bi bayan wani dan takara daga arewacin Najeriya ba.
The Punch ta ruwaito ta rahoto cewa Lalong ya yi wannan ikirarin ne a Jos, lokacin da Amaechi ya je jihar don jan hankalin wakilan jam’iyyarsu yayin da zaben fidda gwani ya ke kunno kai.
Asali: Legit.ng