Yanke Wa Mutane Lantarki Ba Tare Da Ba Su Gargadin Kwana 10 Ba Ya Saba Wa Doka – FCCPC

Yanke Wa Mutane Lantarki Ba Tare Da Ba Su Gargadin Kwana 10 Ba Ya Saba Wa Doka – FCCPC

  • Hukumar Kula da Gasa da Kare Hakkin Masu Sayen Kaya ta Kasa (FCCPC) ta ce yanke wa mutane wutar lantarki ba tare da ba su gargadin kwana 10 ba ya saba doka
  • Mataimakin Shugaban Hukumar FCCPC yace kamfanin rarraba wuta na Kuros Ribas PHEDC ba sa karban kudin wuta a hannun jama'a yadda ya kamata
  • FCCPC ta ce bai kamata kamfanin rarraba wutar lanatarki tana sa mutane siyan na'urorin raba wutan Lantarki a lokacin da suka lalace ba

Jihar Kuros Ribas - Yanke wutar Lantarkin mutanen da ba su biya kudi ba ba tare da ba su gargadin kwana goma daga kamfanonin rarraba wuta na DISCO ya sabawa doka inji hukumar Hukumar Kula da Gasa da Kare Hakkin Masu Sayen Kaya ta Kasa (FCCPC).Rahoton Aminiya. DailyTrust

Kara karanta wannan

Zai iya yin abin da ya ga da: FG ta fadi dalilin da yasa Buhari zai ba 'yan Nijar motocin N1.5bn

Babatunde Irukera, Mataimakin Shugaban Hukumar FCCPC, ya bayyana haka ne a wani shirin warware korafin masu amfani da wutar lantarki da hukumar FCCPC ta shirya a jihar Kuros Ribas.

Babatunde Irukera ya ce binciken su ya nuna Kamfanin Rarraba Hasken Wutar Lantraki ta Fatakwal (PHEDC) bata karban kudin wutar lantarki daga hannun mutane yadda ya kamata.

Bayan haka mutane da dama a yankin sun kawo musu kukan su akan yadda suke yanke musu wutar lantarki ba tare da dokar da kasa ta tsara ba.

PHCNN
Yanke Wa Mutane Lantarki Ba Tare Da Ba Su Gargadin Kwana 10 Ba Saba Wa Doka – FCCPC FOTO PUNCH
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mataimakin Shugaban Hukumar FCCPC ya ce, duk kasuwancin da ya kasa gamsar da kwastomomin sa, kuma yasa su dole su biya kudin wuta ba tare da sun samu wutar ba ta dalilin wani na’ura ya lalace ko wani abu kamar haka, ya sabawa dokar Najeriya.

Babatunde ya ce bai dace ba kamfanin PHEDC ta rika sa yan Unguwa amfani da kudinsu wajen siyan na’urorin rarraba wutar lantarkin da suka lalace kuma bayan haka su karbe iko da su.

Kara karanta wannan

2023: Kungiyar Kirista Ta Watsa Wa CAN Kasa A Ido, Ta Ce Ba Laifi Bane Tinubu Ya Zabi Mataimaki Musulmi

Mijina Ya Boye a Ban Daki Ya Barni A Hannun Yan Fashi Da Makami - Wata Mata ta Fadawa kotu

A wani labari kuma, Wata mata mai suna Asiata Oladejo, ta shaida wa kotun al’ada ta Mapo a garin Ibadan cewa ta raba aurenta a kan dalilin mijinta, Abidemi ya gudu ya bar ta a hannun ‘yan fashi da makami. Rahoton VANGUARD

Oladejo Asiata ta bayyana hakan ne jiya a kotu yayin da mijinta ya shigar da karar ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa