Da Yuwuwar Mai Zai Kara Karanci a Abuja Nan Ba Da Jimawa Ba, Yan Kasuwa
- Da yuwuwar nan ba da jimawa za'a sake shiga wahalhalun ƙarancin Man Fetur a birnin tarayya Abuja
- Wasu bayanai daga ƙungiyoyin yan kasuwa sun nuna cewa Direbobin sun ƙi ɗaukar Man saboda ɓacin hanyar Abuja
- Yan kasuwan Man Fetur sun koka kan yadda kuɗin ɗaukar Mai a jirgin ruwa zuwa wasu jihohi ya tashi
Abuja - Da alamun nan ba da jimawa ba mazauna babban birnin tarayya Abuja zasu ƙara shiga matsanancin halin ƙarancin man fetur.
Jaridar Punch ta tattaro cewa Direbobin Tankoki sun ƙi yarda su ɗauki Mai zuwa birnin saboda rashin kyaun hanya da kuma tsadar Man Dizel.
Kungiyar yan kasuwa masu zaman kansu da yan kasuwar Man Fetur ne suka bayyana haka ranar Talata. Sun ce akwai Mai a ƙasa kamar yadda NNPP ta alƙawarta amma mambobin kungiyar masu dakon Man NARTO ba su shirya zuwa Abujan ba.
Haka zalika, wasu bayanai sun nuna cewa mambobin NARTO sun yi asarar abinda bai gaza Tankoki Bakwai ba duk maƙare da Man Fetur sakamakon rashin kyaun hanyar Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Zuwa ranar Talata, yan kasuwa a shirye suke su biya miliyan N1.2M domin kai musu kaya Abuja, amma babu Direban da ya shirya sa rayuwarsa da Tankarsa kan hanyar, akwai Mai amma Direbobi ba su da nufin zuwa," a cewar wata majiya dake tare da DAPPMAN.
Yan kasuwa sun koka
Bayan haka, yan kasuwan sun koka kan yadda farashin shigo da kayayyaki ya ƙara tashi. Majiyar ƙungiyar DAPPMAN ta ƙara da cewa:
"Lokacin da aka kara farashin Fetur ana canjin Dala tsakanin N600-N620 Amma yanzu ta kai N700. Kuɗin ɗaukar Jirgin ruwa ya kai dala $50,000 a kowace rana haɗi da Motocin NNPC."
"Yana cin sama da $50,000 a kowace rana wajen kai Fetur zuwa jihohi kamar Kalaba, kuma har yau muna biyan kuɗin jirgin ruwa a dalar Amurka."
Wata majiya a ƙungiyar yan kasuwan Man Fetur IPMAN ta faɗi makamancin abinda ta DAPPMAN ta faɗa, inda ta jaddada cewa Direbobin ba su sha'awar ɗaukar kaya daga Warri zuwa Abuja saboda lalacewar hanya.
Shugabann ƙungiyar Direbobin NARTO, Aloga Ignatius, da aka tuntuɓe shi ya ƙi cewa komai kan lamarin, ya nemi a tura masa sakon kuma bai ba da amsa ba har yanzu.
Ya kamata Najeriya ta shiga zamani
Wani Farfesa a fannin tattali a jami'air Uyo, jihar Akwa Ibom, Akpan Ekpo, ya shawarci gwamnatin tarayya ta koma amfani da jrigin ƙasa maimakon Tankoki a matsayin hanyar safarar Man Fetur.
Farfesan ya ce:
"Idan matsalar Direbobi ta ƙi karewa zai jawo ƙarancin Mai, sakamakon haka Farashi ya tashi. Faruwar hakan ba abu ne mai kyau ga tattalin arzikin mu ba domin zai shafi GDP da kuma tashin farashin kayayyaki."
"Ya kamata Najeriya ta soma amfani da jiragen kasa wajen safarar kayan Mai, amfani da Tanka tsohon ya yi ne. Kuma ya kamata a gyara hanyar cikin ƙanƙanin lokaci."
A wani labarin kuma Gwamnatin shugaban ƙasa Buhari ta tabbatar wa yan Najeriya cewa ba abinda zai hana zaɓen 2023
Ministan yaɗa labarai da Al'adu, Lai Muhammed, bayan taro da Buhari ya ce gwamnati zata dawo da zaman lafiya a ƙasa.
Wannan na zuwa ne yayin da wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu suka fara nuna shakku kan yuwuwar zaɓen 2023 saboda rashin tsaro.
Asali: Legit.ng