Bidiyon yadda aka raba kiret ɗin kwai da sunƙin biredi a wani biki ya birge jama'a

Bidiyon yadda aka raba kiret ɗin kwai da sunƙin biredi a wani biki ya birge jama'a

  • Bukukuwa akwai dadi amma bikin kabilar Yarabawa ya kasance na gani da fadi idan aka yi batun hasafi da kyautuka
  • Bidiyon wasu kyautukan biki da aka raba a cikin kwanakin nan sun janyo cece-kuce da jinjina a kafafen sada zumuntar zamani
  • Kiret din kwai da sunkin biredi ba dole ya zamo kyautar bikin da yafi komai ba, amma a halin da kasar nan ta shiga, 'yan Najeriya sun yaba da ita

A yayin da farashin kayayyaki suke cigaba da tashi, jama'a dake raba kyautuka a bukukuwa na cigaba da duba irin kyautukan da zasu bayar domin saukaka rayuwar jama'a.

A wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumuntar zamani, bakin wani bikin Yarabawa sun koma gida da kayan karin kumallo a matsayin kyautar halartar wani biki.

Owambe
Bidiyon yadda aka raba kiret ɗin kwai da sunƙin biredi a wani biki ya birge jama'a. Hoto daga @instablog9ja
Asali: Instagram

Manyan sunkin biredin da aka zuba a wani kwando an dinga mika su ga baki a tebura daban-daban tare da kwayaye da aka shirya su a kananan kiret duk a matsayin kyauta.

Kara karanta wannan

Bidiyon Shugaban APC na Kasa, Sanata Adamu, a Mimbarin Coci yana ihun 'Ku Yabi Ubangiji' ya janyo cece-kuce

Kalla bidiyon a kasa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan Najeriya sun yi martani

Superwoman9ja: "Wannan hadin ya bayar da ma'ana."
Benny_lee04: "Sun yi kokari, saboda biredi da kwai sun zama abinda suka zama a kasuwa."
symplychi_oma: "Sun yi tunani kuwa... Yunwa tayi yawa."
wrldprincecharming: "Zaku ci ko ba za ku ci ba."
sohigh_xy: "Komai na iya tafiya a bikin yarabawa, an taba bani agada."
callmedamy: "Ai ban san liyafar yarabawa bace... Na yarda da mutanena."
Opeyemiadelerin: "A halin da kasar nan ke ciki? Zan iya fara kukan dadi idan aka raba wannan kyautukan ina wurin."

Biki ya yi biki: Bidiyon yadda amarya tayi jifa da gwargwaro da takalmi tana cashewa a bikinta

A wani labari na daban, bidiyon wata amarya tana girgijewa tare da cashewa bayan an saka wakar Kizz Daniels ta Buga a ranar aurenta ya yadu a kafafen sada zumuntar zamani.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Wata Amarya Da Mahaifinta Suka Fashe Da Kuka A Wajen Liyafar Bikinta

A bidiyon mai ban sha'awa, amaryar dake sanye da kayan alfarma amma na gargajiya ta dinga rawan Buga cike da farin ciki tare da annashuwa.

A yayin rawan, amaryar dake cike da murna ta cire takalmanta kuma hakan ya matukar birge bakin dake rawa tare da ita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng