'Yan Bindiga Sun Kai Hari Garuruwa Uku A Jihar Shugaban Ƙasa, Sun Kashe Rayuka
- Miyagun yan bindiga sun sake kai sabon hari ƙauyuka uku a jihar Katsina, sun yi ta'adi ba tare da samun tirjiya ba
- Mazauna ƙauyukan da abun ya shafa sun yi ikirarin cewa sun kira hukumomin tsaro yayin harin amma ba'a ɗauka ba
- Katsina na ɗaya daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ke fama da ayyukan ta'addancin yan bindiga
Katsina - Aƙalla mutum biyu suka rasa rayukan su, wasu Takwas aka yi garkuwa da su, yayin da wasu yan bindiga suka kai hari ƙauyuƙa ranar Lahadi da daddare a jihar Katsina.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa maharan sun kai sabon hari Ƙauyukan Babbar Ruga, Kwarin Maikotso da kuma Kore, inda suka ci karen su babu babbaka, suka sace dabbobi.
Mazauna sun bayyana cewa yan fashin dajin da suka kai adadin mutum 10 kowane ɗauke da bindigar AK-47 sun farmaki ƙauyen Babbar Ruga da misalin ƙarfe 2:00 na tsakar daren Lahadi.
Harin wanda ya kasance karo na biyu a ƙauyen, yan bindigan sun sace mutum biyu amma ɗaya daga ciki ya samu nasarar gudo wa daga hannun su.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Legit.ng Hausa ta gano cewa ƙauyen na da nisan kilo mita uku kacal zuwa kwaryar birnin Katsina, babban birnin jihar.
A ƙauyukan Kwarin Maikotso da Kore, waɗan da tsakanin su da Babbar Ruga bai wuce tafiyar kilo mita Bakwai ba, maharan sun halaka rayukan mutum biyu.
Bayan haka, yan ta'addan sun yi gaba da mutane Bakwai da adadi mai yawa na dabbobi a ƙauyukan biyu yayin harin, wanda basu samu tirjiya daga jami'an tsaro ba.
Wane mataki mutane suka ɗauka?
Mazauna ƙauyukan da abun ya shafa sun yi ikirarin cewa sun kira layukan gaggawa na hukumomin tsaro yayin harin amma ba bu martani.
Duk wani yunkurin jin ta bakin hukumar yan sandan jihar ya ci tura kasancewar kakakin yan sanda, SP Gambo Isa, bai ɗaga kira ba kuma bai turo amsoshin sakonnin da muka aika masa ba.
Wani mazaunin cikin garin Katsina, Abdullahi Muhammad, ya tabbatar wa wakilin Legit.ng Hausa da kai hari kauyen Babbar Ruga, inda ya ce abun tashin hankali ne gare su.
Muhammd ya ce bayan samun labarin, ya kira ta wayar salula ƙauyen kuma an tabbatar masa yan bindiga sun shiga sun aikata ta'asa a ƙauyen.
Ya ce:
"Babban Ruga ba ta da nisa da Katsina, bai wuce kilomita biyu ko uku, ƙauyen na kusa da Makarantar horar da jami'an Cibil Defence watau NSCDC."
A wani labarin kuma Gwamna Tambuwal Ya Karbi Rahoton Rikicin Da Ya Jawo Kisan Deborah Samuel, Ɗalibar da ta zagi Annabi SAW
Gwamna Aminu Tambuwal ya karɓi rahoton kwamitin da gwamnatinsa ta kafa kan rikicin kisan Deborah Samuel a Sokoto.
Yayin tabbatar da nufin gwamnatinsa na aiwatar da shawarin kwamitin, Tambuwal ya ce zai kawo karshen faruwar lamarin a Sokoto.
Asali: Legit.ng