Gwamna Tambuwal Ya Karbi Rahoton Rikicin Da Ya Jawo Kisan Deborah Samuel

Gwamna Tambuwal Ya Karbi Rahoton Rikicin Da Ya Jawo Kisan Deborah Samuel

  • Gwamna Aminu Tambuwal ya karɓi rahoton kwamitin da gwamnatinsa ta kafa kan rikicin kisan Deborah Samuel a Sokoto
  • Yayin tabbatar da nufin gwamnatinsa na aiwatar da shawarin kwamitin, Tambuwal ya ce zai kawo karshen faruwar lamarin a Sokoto
  • Fusatattun matasa da ɗalibai sun ƙashe Deborah ne bayan da aka zarge ta da yin munanan kalamai ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad SAW

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Sokoto - Kwamitin da gwamnatin jihar Sakkwato ta kafa domin ya binciko ainihin tashin hankalin da ya faru ranar 12 ga watan Mayu, 2022 a kwalejin Shehu Shagari ya miƙa rahotonsa ga Gwamna Aminu Waziri Tambuwal.

Tambuwal, bayan karɓan rahoton ya bayyana kiraye-kirayen da masu ruwa da tsaki ke yi na buɗe kwalejin, a cewarsa gwamnatinsa zata duba yuwuwar yin hakan.

Gwamna Tambuwal daga Hagu, Deborah a dama.
Gwamna Tambuwal Ya Karbi Rahoton Rikicin Da Ya Jawo Kisan Deborah Samuel Hoto: the nation
Asali: UGC

The Nation ta tattaro cewa gwamnan ya umarci hukumar makarantar ta kira taro na musamman, wanda zai maida hankali kan shirye-shiryen yadda za'a cigaba da karatu.

Kara karanta wannan

Kwamishinan Gwamnan Arewa Ya Bi Sahun Wasu Jiga-Jigan PDP, Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC

Wane mataki Gwamnati zata ɗauka Kan rahoton?

Da yake tabbatar wa mutane cewa gwamnatinsa zata aiwatar da shawarwarin kwamitin, gwamna Tambuwal ya ce yin hakan zai kare faruwar makamancin abinda ya faru nan gaba, ba a kwalejin kaɗai ba har da sauran makarantu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wata sanarwa da mai taimaka masa ta fannin yada labarai, Muhammad Bello, ya fitar, ta yi roko ga gwamnatin tarayya da ƙungiyar Malaman Jami'o'i su zubar da wukaken su, su cimma matsayar da zata kawo ƙarshen yajin aiki.

"Ba abun da ya fi karfin yin sulhu, Wajibi duba da goben yayan mu da ƙasar mu, mu lalubo maslaha. Akwai ungo da karɓi a tattaunawar sulhu, saboda haka ASUU da FG ya dace ku aje ra'ayoyin ku domin ɗalibai su koma aji."

A wani labarin kuma Mahaifiyar Deborah Samuel ta bayyana cewa ba zata taɓa mancewa da ranar mutuwar ɗiyarta ba

Kara karanta wannan

Sheikh Bello Yabo ya fusata, ya roki Allah yasa a sace Buhari, El-Rufai da Garba Shehu

Mahaifiyar ɗalibar makarantar Kwaleji ta Shehu Shagari, Deborah Samuel, wacce aka kashe da zargin ɓatanci ta faɗi halin da ta shiga.

Matar mai suna, Alheri Emmanuel, ta ce ta samu labarin kisan ɗiyarta ta bakin ƙawayenta kuma ba zata taɓa mance wa da ranar ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel