Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Ya Koka Kan Tsadar Rayuwa, A Yayin Da Farashin Kaya Ke Cigaba da Tashi A Kasar
- Bisa alamu tsadar rayuwa a kasar ya fara taba kowane dan kasar ciki har da tsohon shugaban kasa
- Olusegun Obasanjo ya ce kallubalen tsadar rayuwa da kasar ke fuskanta ya fara shafansa musamman a gonarsa na kifi
- A cewar tsohon shugaban kasar, rashin shugabanci na gari ne ya janyo kunci da wahalhalun da yan Najeriya suka tsinci kansu a yau
Tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya Olusegun Obasanjo a ranar Talata 2 ga watan Agusta ya shiga jerin miliyoyin yan Najariya da ke kokawa kan tsadar rayuwa da wasu abubuwan.
Obasanjo ya bayyana cewa yana keta gumi sosai saboda tsadar dizal wanda ke shafar kasuwancinsa da wasu kasuwancin a sassan kasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daily Trust ta rahoto cewa tsohon shugaban kasar ya yi wannan jawabin ne a wurin taron masu kiwon kifi na kudu maso yamma da aka yi a dakin karatu na Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo (OOPL) a Abeokuta, Jihar Ogun.
Yayin da ya ke kokawa kan tsadar dizal, da kuma tashin farashin abincin kifi, Obasanjo ya ce manoman Najeriya za su rasa ayyukansu idan lamarin ya cigaba a haka.
Ya kara da cewa idan ba su (manoman) sun taru sun tsayar da farashi guda ba da za su rika sayar da kayansu; abubuwa za su fi karfinsu.
Kalamansa:
"Farashin dizal ya tashi saboda shugabancin kasar nan baya tafiya yadda ya kamata. Wannan shine dalili.
"Kuma, abin da zai faru shine, musamman mu da ke amfani da dizal wurin noman kifi, kasuwancin mu za ta rushe, kuma ko hakan ya faru, dole yan Najeriya su ci abinci.
"Noman kifi zai gagari mutane a lokacin, wasu za su rika noman kifi daga kasashen waje su kawo mana nan.
"Kuma za ku rassa ayyukan ku, ku talauce. Don haka, mene za mu yi? Mu hada kai ... Muna son cigaba da noman kifi kuma dole mu kula da wadanda za su ci kifin da mu masu noman."
Babban tambaya ga manoman kifi a Najeriya
Da ya juya ga manoman, Obasanjo ya tambaya:
"Su wane cikin ku ke amfani da dizal wurin noma? Domin ina amfani da dizal kuma tuni na fara gumi. Gumi na keto min."
"Bisa Tsautsayi Na Zama Shugaban Najeriya", Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo
A wani rahoton, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce duk abubuwan da ya aikata da ya kuma samu bisa tsautsayi ne amma banda noma, rahoton PM News.
Tsohon shugaban na mulkin soja, wanda aka zaba a karkashin mulkin farar hula a 1999, ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 23 ga watan Yuli, a wani shirin rediyo na kai tsaye tare da Segun Odegbami a Eagles 7 Sports 103.7 FM, Abeokuta.
Asali: Legit.ng