Yanzu-Yanzu: Fitaccen Dan Siyasan Arewa Ya Mutu A Hatsarin Mota
- Allah ya yi wa kwamishinan matasa da wasanni na Jihar Yobe, Honarabul Goni Bukar Lawan wanda aka fi sani da BUGON rasuwa
- Tsohon dan majalisar tarayyar ya rasu ne sakamakon hatsarin mota da ya ritsa da shi a hanyar Damaturu zuwa Kano a daren ranar Talata 2 ga watan Agusta
- Rahotanni sun bayyana cewa mamacin ya hallarci wata jana'iza ne a garin Damaturu a ranar Talatar amma shima Allah ya masa rasuwa a hanyarsa na tafiya
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jihar Yobe - Kwamishinan Matasa Da Wasanni na Jihar Yobe, Hon. Goni Bukar Lawan, (BUGON) ya mutu a hatsarin mota kan hanyar Damaturu zuwa Kano.
Goni Bukar, tsohon dan majalisar wakilai na tarayya, wanda aka fi sani da BUGOM, ya rasu a daren yau Talata a hanyarsa na zuwa Jihar Kano, Leadership ta rahoto.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jaridar ta ambaci majiya na cewa mamacin ya hallarci jana'iza a Damaturu babban birnin Jihar Yobe a yammacin ranar Talata, kafin ya kama hanyar zuwa Jihar Kano.
Za a yi jana'izarsa a ranar Laraba a Damaturu domin an koma da gawarsa Damaturu babban birnin jihar Yobe a daren ranar Talata, Daily Indepedent ita ma ta rahoto.
Ya rasu ya bar mata biyu da yara.
Allah Ya Yi Wa Tsohon Shugaban Rikon Kwarya Na BUK Rasuwa
A wani rahoton, tsohon shugaban rikon kwarya na Jami'ar Bayero ta Kano, BUK, Farfesa Danjuma Maiwada, ya rasu yana da shekaru 70 a duniya, Daily Trust ta ruwaito.
Maiwada, wanda ya yi aiki na kankanin lokaci a matsayin shugaban riko na BUK a 2004, dan asalin Jihar Katsina ne amma mafi rayuwarsa a Kano ne inda ya ke koyarwa a jami'ar tun 1976 a tsangayar ilimi.
A shekarar 2015, ya yi aiki a matsayin shugaban riko na jami'an Northwest University, Kano da yanzu ake kira Jami'ar Yusuf Maitama Sule.
Yana daga cikin masu fada a ji a tsangayar koyar da manya da ilimin addinin musulunci kuma ya koyar da malamai ciki har da shugaban jami'an na yanzu, Farfesa Sagir Adamu Abbas.
Asali: Legit.ng