Gwamnatin Ganduje ta bukaci a ruguza wani gini a kusa da gidan Sheikh Kabara
- An daura wani gini a kusa da gidan Shehin malamin addinin musuluncin da aka yi, Nasiru Kabara
- A yau ne aka ji Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta bada umarnin gaggauta rusa wannan gini
- KAROTA tana zargin an fara daura wannan ginin ne ba tare da izinin Gwamnati ko Masarauta ba
Kano - Gwamnatin jihar Kano ta bukaci a gaggauta rusa wani gini da aka yi ba tare da bin ka’ida ba a kusa da gidan Sheikh Nasiru Kabara da ke jihar Kano.
Mai girma Abdullahi Umar Ganduje ya bada wannan umarni ne bayan bincike ya nuna masa an daura ginin ne ba tare da an samu umarni daga hukuma ba.
A ranar Talata, 2 ga watan Agusta 2022, jaridar Daily Trust ta kasar nan ta rahoto cewa masarautar jihar Kano ce ta mallaki wannan filin da ake tababa a kai.
Shugaban hukumar KAROTA na Kano, Hon. Baffa Ɗan’agundi yace gwamnatin jiha da masarautar Kano duk ba su bada umarni kafin a fara wannan ginin ba.
KAROTA ta fitar da jawabi
An fahimci hakan ne a wani jawabi da kakakin hukumar KAROTA, Nabilusi Abubakar ya fitar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Lamarin har ya kai zargi ya shiga tsakanin Gwamnatin Abdullahi Ganduje da kuma masarauta a karkashin jagorancin Mai martaba, Alhaji Aminu Ado Bayero.
“Yana da muhimmanci a fahimci wannan haramtaccen gini ya haddasa zargi tsakanin gwamnatin jiha da masarauta.”
“An fahimci wasu hadamammu da mutane masu son rai da wadanda kansu kurum suka sani ne suke da hannu wajen gini."
“Ana cigaba da gudanar da bincike, kuma gwamna ya bada umarni a ruguza katanga da ginin wajen wasan yara da aka daura.”
“Sannan za a katange ragowar filin da mabiya darikar Kadiriyya suke amfani da shi wajen ibada na ambaton Ubangiji (zikiri).”
- Shugaban KAROTA
A jawabin da ya fito da yammacin yau, an ji cewa Gwamna Ganduje ya bada umarni a baza jami’an tsaro dare da rana a wurin domin kare lafiyar yara da iyaye.
Daily Nigerian ta rahoto cewa Honarabul Dan’agundi shi ne shugaban kwamitin da yake da alhakin kauda ginin da ya saba doka, ya kuma gargadi jama'a.
Za a tsige Buhari?
A baya an ji labari Sanata Adamu Muhammad Bulkachuwa ya bayyana dalilin Majalisa na kawo shawarar a tunbuke Mai girma Muhammadu Buhari.
‘Dan Majalisar yace babu abin da Sanatoci ba suyi ba domin a samu zaman lafiya amma abin ya gagara, sai suka bijiro da batun tunbuke shugaban kasar.
Asali: Legit.ng