Rashin tsaro: FRSC za ta fara kame baburan da ba su da rajista a fadin Najeriya

Rashin tsaro: FRSC za ta fara kame baburan da ba su da rajista a fadin Najeriya

  • Hukumar kula da haddura ta kasa ta bayyana bukatar fara dakile zirga-zirgar babura masu kada biyu marasa rajista a kasar nan
  • Hukumar ta ce za ta hada kai da hukumomin tsaro da hukumar kudaden shiga a jihohi don tabbatar da hakan
  • An samu cece-kuce tsakanin 'yan Najeriya a baya-bayan nan bayan bijiro da batun dakatar da kabu-kabu a kasar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - A ci gaba da kokarin dakile matsalar rashin tsaro a kasar nan, hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), ta yanke shawarar daukar tsauraran matakai kan baburan da ba su da rajista a fadin jihohi 36 na tarayyar kasar nan.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in kula da harkokin jama’a na hukumar , ACM, Bisi Kazeem, a ranar Litinin, a Abuja, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da mazauna Abuja suka dage dole Buhari ya sauke ministansa da mai ba shi shawara

Za a fara kama babura marasa rajista a Najeriya
Rashin tsaro: Hukumar FRSC za ta dakile baburan da ba su da rajista ba | Hoto: Nnenna Ibeh, Legit.ng

Sanarwar ta umurci dukkanin kwamandojin hukumar FRSC 37 da su gaggauta kame duk wani babur da aka gani ba tare da rajista ba.

Hakan dai na zuwa ne kamar yadda sanarwar ta ce, an yanke shawarin ne don tabbatar da cewa an adana bayanan dukkan ababen hawa masu kafa biyu a kundin tsarin tantance ababen hawa na kasa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Manufar gwamnati kan wannan batu

A cewar sanarwar, umarnin ya zo ne biyo bayan bukatar da ake da ita na bin umarnin gwamnatin tarayya don dakile wadannan tarkacen baburan da ba su da rajista a kan titunan Najeriya.

A cewar wani yanki na sanarwar:

“Abin da ya sa ake fama da matsalar rashin tsaro ne ya sa aka ba da umarnin dakatar da zirga-zirgar wadannan nau’ukan ababen hawa da ba su da rajista a hanyoyinmu."

Jairdar The Nation ta ce, sanarwar ta kara da cewa, za a gaggauta hada kai da hukumar tattara kudaden shiga na jihohi, tare da kafa wata runduna ta hadin gwiwa da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro don tabbatar da dokar.

Kara karanta wannan

An samu ci gaba: Minista Pantami ya haramta shigo da layukan waya daga kasashen waje

Gwamnati Ta Haramta Yin Acaba a Ƙananan Hukumomi 6 a Legas

A wani labarin, gwamnatin Jihar Legas ta haramta yin haya da babur wato acaba a kananan hukumomi shida na jihar, rahoton Channels Television.

Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Legas ne ya sanar da hakan yayin da ya ke yi wa hukumomin tsaro a jihar jawabi a ranar Laraba, rahoton The Cable.

Kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Ikeja, Surulere, Eti Osa, Lagos Mainland, Lagos Island da Apapa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.