Ci gaba: Minista Pantami ya haramta shigo da layukan waya daga kasashen waje

Ci gaba: Minista Pantami ya haramta shigo da layukan waya daga kasashen waje

  • Gwamnatin Buhari ta bayyana kawo karshen shigo da layukan SIM zuwa Najeriya saboda wasu dalilai na ci gaba
  • Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani ya bayyana cewa, kawo karshen layukan kasashen waje zai taimakawa ci gaban Najeriya
  • Hakazalika, gwamnati ta ce an gina kamfanin da zai ke samar da akalla layuka miliyan 200 a duk shekara a jihar Legas

Jihar Legas - A ranar Litinin ne muke samun labarin cewa, gwamnatin tarayya ta sanar da hana shigo da layukan waya da aka fi sani da SIM a kasar.

Ministan sadarwa da tattalin arzikin dijital na kasar Farfesa Isa Pantami ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a birnin Legas.

Gwamnatin Buhari ta kawo karshen siyo layukan waya daga kasashen waje
Ci gaba: Minista Pantami ya haramta shigo da layukan waya daga kasashen waje | Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Jaridar PM News ta ce, Pantami ya bayyana haka ne a wajen bikin baje kolin kamfanonin sadarwa na kasa (NTICE) wanda ofishin bunkasa fasahar sadarwa ta Najeriya (NODITS) na Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ya shirya. .

Ministan ya bayyana karara cewa gwamnati ba za ta kara lamunta da shigo da layukan SIM cikin kasar nan ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Pantami ya bayyana cewa yanzu haka al'ummar kasar na kera layukan waya na SIM a cikin gida, don haka babu bukatar ci gaba da shigo da na waje.

A cewarsa, manufar kasar ita ce a kara samar da abubuwan cikin gida a fannin ICT ta yadda nan da 2025 al’ummar kasar za su dogara da kansu da akalla 80% cikin dari na kayayyakin cikin gida.

A taimaki gwamnati ta cimma burin samar da kayayyakin cikin gida, Pantami

Pantami ya bukaci masu ruwa da tsaki da ’yan kasa da su tallafa wa kokarin gwamnati na bunkasa samar da kayayyakin cikin gida.

A cewarsa, kamar yadda jaridar BluePrint ta ruwaito:

"Idan muka yi haka, tarihi zai tuna da mu da alheri."

A watan Yunin da ya gabata, Pantami ya sanar da jama’a cewa gwamnatin Buhari ta kafa kamfanin kera layukan SIM a jihar Legas.

Aikin na gwamnati, wanda aka gina tare da tallafin wani kamfani mai zaman kansa, yana da ikon samar da katunan SIM miliyan 200 a duk shekara tare da fitar da su zuwa wasu kasashen Afirka.

Bidiyon karamar yarinya dake kaunar Sheikh Pantami, ministan ya sha alwashin tuntubar danginta

A wani labarin, bidiyon wata karamar yarinya wacce aka bayyana sunanta da Rukayya dake kaunar Sheikh Ali Isah Pantami ya bayyana.

A bidiyon da 'yar uwar yarinyar mai amfani da sunan @Miss_Luthor ta saki a shafinta na Twitter tare da janyo hankali ministan ta hanyar kiran sunansa, ta sanar da irin kaunar da yarinyar ke wa ministan.

A wallafarta: "Salam, 'yata mai suna Rukayya tana matukar kaunar Sheikh Pantami. Duk lokacin da taji muryarsa a talabijin, a guje take zuwa tana ihun "Sheikh Pantani". Ta rubuta masa wasika kuma ta sa hannu a kai da kanta."

Asali: Legit.ng

Online view pixel