Ta'addanci: Mazauna Abuja sun yi zanga-zanga, sun nemi Buhari ya tsige Ministan Tsaro da NSA

Ta'addanci: Mazauna Abuja sun yi zanga-zanga, sun nemi Buhari ya tsige Ministan Tsaro da NSA

  • Mazauna babban binrin tarayya Abuja sun fito zanga-zangar neman zaman lafiya a birnin da shugabancin kasar ke zaune
  • Mazauna sun fito kwai da kwarkwata domin nuna fushi, suka kuma bukaci Buhari ya tsige Ministan tsaro da mai ba shi shawari kan harkokin tsaro
  • Makwanni kadan da suka gabata ne aka samu faruwar hare-hare kan mazauna da jami'an tsaron gwamnati a birnin

FCT, Abuja - A ranar Litinin ne dimbin mazauna Abuja suka yi dandazo a dandalin Unity Fountain na birnin domin nuna rashin amincewarsu da karuwar rashin tsaro da rashin tabuka komai daga jami’an tsaro wajen dakile ta’addancin garkuwa da mutane.

Babban birnin tarayya Abuja ya shiga sahun wuraren da ke fama da yawaitar hare-haren 'yan ta'adda a cikin shekarar nan, inda aka samu munanan hare-hare da dama, This Day ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Duk sace N109bn na kasa, kotu ta ba da belin akanta janar da shugaba Buhari ya dakatar

An dage Buhari ya sake wasu da suka gaza magance tsaro a Najeriya
Ta'addanci: Mazauna Abuja sun yi zanga-zanga, suna neman Buhari ya tsige Ministan Tsaro da NSA | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Da suke jawabi a karkashin kungiyar masu kula da harkokin dimokaradiyya ta GDDI, matasan da suka fusata sun yi mamakin dalilin da ya sa duk da rahotannin sirri da aka samu na wasu shirye-shiryen kai hare-hare a Abuja, har yanzu ba a samu mafita ba.

Sun kuma nuna fushi da harin da aka kai gidan yarin Kuje inda aka kubutar da kwamandojin 'yan ta'adda 66, Vanguard ta ruwaito.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Abin da muke so Buhari ya yi

A bangare guda, sun ce sun fahimci cewa, Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi (rtd), da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (rtd) ba za su iya tsinana komai ba.

Don haka, daya daga cikin shugaban kungiyar, Kwamared Danesi Momoh, ya ce ya kamata shugaban kasa Muhammadu Buhari, nan take ya sallami mai ba shi shawara kan harkokin tsaro (NSA), Manjo Janar Babagana Monguno (Rtd).

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Buhari ya yi martani kan barazanar tsige shi da sanatocin PDP suka yi

Hakazalika, sun nemi ya sallami Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi (Rtd), saboda rashin sanin makamar aikinsu wajen tunkarar kalubalen tsaro da ke ruguza kasar nan.

Masu zanga-zangar da suka zagaya kan titunan Abuja, an gansu dauke da kwalaye da dama na neman shugaban kasa ya sauke Janar Monguno da Magashi daga mukamansu tare da maye gurbinsu da kwararrun jami’an tsaro.

Kungiyar ta yi gargadin cewa idan har Shugaba Buhari ya gaza kuma yayi kunnen uwar shegu da kiran nasu, to babu abin da zai rage musu illa hada karfi da karfe da masu neman ya sauka daga mulki ko kuma a tsige shi shi kansa.

Harin Bwari: Sojojin Najeriya sun kashe 'yan ta'adda 30 da suka kai kan sojoji fadar Buhari

A wani labarin, rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da ragargazar wasu 'yan ta'adda 30 da ake zargin sun kai hari kan sojojin fadar shugaban kasa a makon nan.

Kara karanta wannan

Akwai Zagon Kasa A Cikin Harin Da Aka Kaiwa Dakarun Sojojin Guards Brigade a Abuja - Sojoji

Rahotanni a baya sun bayyana cewa, an kai hari kan sojojin Najeriya a Abuja, inda aka hallaka jami'ai uku tare da jikkata wasu.

Daraktan yada labarai na tsaro, Bernard Onyeuko ya bayyana aikin da jami'an suka yi a wani taron manema labarai na mako bibbiyu kan ayyukan tsaro a ranar Alhamis a Abuja, rahoton Daily Nigerian.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.